Hukumar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda (PSC), ta dakatar da dan sandan da ake zargi da kashe lauya Bolanle Raheem da bindiga a Legas.
Dakatarwar na kunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar ta bakin shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a, Mista Ikechukwu Ani, ranar Alhamis a Abuja.
Sanarwar ta ce dakatarwar da aka yi wa jami’in ta fara aiki ne take ba da bata lokaci ba.
Haka nan, hukumar ta ba da umarnin a yi binciken karshe kan badakalar domin daukar mataki na gaba.
Ani ya ce, bayan nazari cikin nutsuwa da hukumar ta yi wa lamarin ta aike wa Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da wasika inda ta samu amincewarsa kan a dakatar da jami’in da lamarin ya shafa ba tare da bata lokaci ba.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito yadda dan sanda ya dirka wa marigayiyar bindiga ranar Kirsimeti a Legas, lamarin da ya ja hankalin jama’a a gida da wajen kasa.