✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Za a binciki NPA bayan dakatar da Hadiza Bala Usman daga shugabancinta

Hakan na zuwa ne bayan sauke Hadiza Bala Usman daga shugabancin hukumar a ranar Alhamis.

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamiti domin binciken Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA).

Matakin dai na zuwa ne jim kadan bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauke Hadiza Bala Usman daga shugabancin hukumar a ranar Alhamis.

Babban Mai Taimakawa Shugaban Kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da kafa kwamitin ranar Alhamis.

Wani hadimi ga Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ma ya tabbatar da hakan ga wakilinmu, ko da yake ya ce har yanzu ba a sanar da hakan ba a hukumance.

To sai dai Garba Shehu a cikin sanarwar tasa ya ce Shugaba Buhari ya amince da kafa kwamitin binciken tare da sauke Hadizan daga kan mukaminta har zuwa lokacin da za a kammala shi.

Sanarwar ta ce, “Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da shawarwarin Ma’aikatar Sufuri karkashin jagorancin Rotimi Amaechi kan kafa kwamiti domin binciken hukumar gudanarwar NPA.

“Shugaban ya kuma amince cewa shugabar hukumar, Hadiza Bala Usman ta sauka daga mukaminta. Yayin da ake gudanar da binciken, Mohammed Koko kuma zai maye gurbinta har zuwa lokacin da za a kammala binciken

“Kwamitin dai zai kasance karkashin jagorancin Darakta mai kula da Sashen Harkokin Jiragen Ruwa, yayin da Mataimakin Darakta a Sashen Shari’a na ma’aikatar zai kasance Sakataren kwamitin. Ministan Sufuri ne zai nada sauran mambobin kwamitin,” inji sanarwar.