✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a bayyana Gwarzon Shekara na Gasar Haddar Al-Kur’ani

Daliba mai shekara 15 na fafatawa a rukunin haddar Izu 60 da Tafsiri

A safiyar Asabar, 27 ga Maris 2021 ake sa ran bayyana Gwaron Shekara na Gasar Karatun Al-Kur’ani ta Kasa Karo na 35 da ke gudana a Jihar Kano.

Mahaddata fiye da 300 a rukuni daban-daban na musabakar daga fadin Najeriya sun kammala fafatawa tare da bajen bajintarsu a ranar Juma’a.

Mahaddatan sun fafata ne a runi shida wanda mafi girman cikinsu shi ne rukunin Izu 60 da Tajwidi da kuma Tafsiri.

Mahaddaciya A’ishatu Kabiru Shu’aibu mai shekara 15 daga Jihar Gombe na daga cikin mafiya jan hankali a wannan rukunin.

Aishatu ita ce mafi karancin shekaru a rukunin masu musabaka a rukunin na mahaddata a Izu 60 da Tafsiri a gasar karo na 35.

Aishatu Kabiru Shu’aibu tare da jami’an musabakar. (Hoto: National Qur’anic Memorization Competition of Nigeria)

Sauran su ne rukuni biyar din su ne rukunin Izu 60 Izu 40, Izu 20, Izu 10 da kuma ’yan Izu biyu.

A ranar Asabar ake sa ran Kwamitin Alkalan Gasar za su sanar da wadanda suka yi zarra a gasar.