A safiyar Asabar, 27 ga Maris 2021 ake sa ran bayyana Gwaron Shekara na Gasar Karatun Al-Kur’ani ta Kasa Karo na 35 da ke gudana a Jihar Kano.
Mahaddata fiye da 300 a rukuni daban-daban na musabakar daga fadin Najeriya sun kammala fafatawa tare da bajen bajintarsu a ranar Juma’a.
- An fitar da sunayen wadanda suka yi nasarar samun NDA
- Shin malaman Kano za su iya ja da Abduljabbar?
- Mun gano masu garkuwa da daliban Kaduna 39 —Gumi
- 2023: Yadda baraka ke karuwa tsakanin Buhari da Tinubu
Mahaddatan sun fafata ne a runi shida wanda mafi girman cikinsu shi ne rukunin Izu 60 da Tajwidi da kuma Tafsiri.
Mahaddaciya A’ishatu Kabiru Shu’aibu mai shekara 15 daga Jihar Gombe na daga cikin mafiya jan hankali a wannan rukunin.
Aishatu ita ce mafi karancin shekaru a rukunin masu musabaka a rukunin na mahaddata a Izu 60 da Tafsiri a gasar karo na 35.
Sauran su ne rukuni biyar din su ne rukunin Izu 60 Izu 40, Izu 20, Izu 10 da kuma ’yan Izu biyu.
A ranar Asabar ake sa ran Kwamitin Alkalan Gasar za su sanar da wadanda suka yi zarra a gasar.