Amurka ta yi alkawarin ladar Dala miliyan goma (kimanin Naira biliyan 3.8) ga duk wanda ya bayar da bayani game da kutsen kasashen waje a zabukanta.
Sakataren Amurka Michael Pompeo ya ce tayin wani yunkuri ne na tadiye kasashen waje da ke yin kutse ta intanet a zabukan kasar.
Batun kutsen intanet a zaben shugaban Amurka na 2016 da ake zargin Rasha ta yi ya haifar da zazzafar muhawara a fagen siyasar Amurka.
A 2019 lauya mai zaman kansa Robert Mueller ya jagoranci binciken zargin Rasha da yi wa Donald Trump magudi ta intanet domin ya ci zabe.
Shugaba Trump ya musanta hada baki da Rasha ya kuma kira binciken na Mueller cuwacuwar da ‘yan jam’iyyar Demokrat suka dauki nauyi.
Rahoton kwamitin Mueller mai shafi 448 ya ce babu tabbacin Trump ya hada baki da Rasha domin sauya sakamakon zaben.
Sai dai ya zargi Trump da yunkurin hana binciken har sau 10, zargin da shi ma Trump din ya musa.
A watan Yuli, dan takarar shugaban kasar Demokrat a zaben watan Nuwamba, Joe Biden ya ce ya samu labarin yunkurin sake hada baki da Rasha.
Biden ya lashi takobin daukar fansa a kan duk kasar da ta nemi yin shisshigi a tsarin zaben Amurka.