✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaɓen shugaban kasa: Yau za a yi ta ta kare a Kotun Koli

Yau ne Kotun Koli za ta yanke hukunci a shari’ar ƙalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.

Yau ne Kotun Koli za ta yanke hukunci a shari’ar ƙalubalantar nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.

Idan Kotun Koli ta soke nasarar Tinubu, zai sama mutum na farko da kotun koli ta ƙwace kujerar shugaban kasa a hannunsa a tarihin Najeriya.

Idan kuma ya yi nasara, zai zama akalla karo na uku da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yake shan kaye a kotun koli a yunkurinsa na darewa a kan kujerar shugaban kasa.

Kwamitin alkalai bakwai na kotun ne za su yanke hukuncin a karkashin karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro.

Sauran alkalan su ne: Uwani Abba-Aji, Lawal Garba, Ibrahim Saulawa, Adamu Jauro, Tijjani Abubakar da kuma Emmanuel Agim.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da takwaransa na Jam’iyyar LP, Peter Obi sun daukaka kara zuwa kotun koli ne saboda rashin gamsuwa da hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaben Shugaban Kasa, wadda ta kori ƙararsu saboda rashin gamsassun hujjoji.

Atiku da Peter Obi, kowannensu na neman kotun koli ta ƙwace kujerar shugaban kasa daga hannun Tinubu, ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u mafiya rinjaye.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairu, aka rantsar da shi 29 ga wata Mayu.

Kotun za ta yi zamanta na ƙarshe ne a bayan wani sabon babi kan dambarwar takardar shaidar karatun Tinubu, wanda Atiku ke zargin sa da amfani da na jabu.

Atiku wanda ke zargin Tinubu da amfani takardar shaidar karatun bogi na Jami’ar Jihar Chicago (CSU), zargin da Tinubun ya musa.

A makonni baya ne Atikun ya samu kwafin takardun daga jami’ar, wanda yake neman gabatarwa a matsayin sabuwar hujja Kotun Koli, amma ɓangaren Tinubu ya ce alkami ya bushe na gabatar da hujjoji, tun da ba a gabatar da su a kotun baya ba.

Za a yi zaman karshen ne kwana uku bayan zaman farko wanda  alƙalin ya bayyana cewa wasikun da suka samu daga Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka kan sahihancin takardun shaidar karatun Tinubu sun yi karo da juna.

Atiku na zargin Tinubu da amfani da takardun CSU bogi, don haka yake neman a kwace kujerar a ba shi.

Sauran bukatun Atiku da Obi su ne, iƙirarin samun kuri’u mafiya rinjaye da kuma yi musu magudi a wasu rumfunan zabe.