Amakon jiya ne, kotunan da aka kafa domin sauraren kararrakin zaben gwamnoni na 2023 suka fara yanke hukunci game da zaben gwamnonin.
A jihohin Bauchi da Filato da Zamfara da Enugu kotunan sun yanke hukuncin cewa gwamnonin da ke kan mulki ne suka yi nasara a zaben da ya gabata.
- Shugabar karamar hukuma ta rushe gidajen Gala 39 a Yobe
- Najeriya@63: Muhimman abubuwa 10 daga jawabin Tinubu
Wannan ya sa magoya bayansu suka barke da sowa da murna ganin gwanayensu sun samu tsallakewa a zagayen farko na shari’ar da aka yi.
Sai dai akwai sauran tsalle, saboda wadanda ba su yi nasara ba suna iya daukaka kara a kan hukuncin, don haka dole su sake shirya lauyoyi domin fuskantar kalubale na gaba.
A bisa doka dai, Kotun koli ce ke zartar da hukunci na karshe game da zaben gwamnoni da na Shugaban kasa, shi ya sa Bahaushe ke yi wa kotun kirarin ‘daga ke sai Allah Ya isa,’ saboda idan ta zartar to bakin alkalami ya riga ya bushe.
Shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano, ta dade da daukar hankalin mutane da yawa a Arewacin Najeriya, domin tana cikin shari’un da ake yawan maganarta a kafafen sada zumunta na zamani musamman a tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da na NNPP mabiya Kwankwasiyya.
Kafin yanke hukuncin da ya zo da ba-zata, kusan kowane bangare na ikirarin shi ne zai samu nasarar wannan shari’a.
Amma gab da za a yanke hukunci kan wannan zabe, alamu sun nuna cewa jikin mabiya Kwankwasiyya ya yi sanyi matuka, sun yi ta zargin cewa za a yi musu rashin gaskiya za a kwace musu gwamnati, wannan ya sanya suka rika gudanar da zanga-zanga da yin salloli don neman agajin Ubangiji a kan shari’ar.
Bugu-da-kari, wani abu na ba kasafai ba da ya sake nuna girman kalubalen da Kwankwasiyya ke fuskanta dangane da shari’ar shi ne, halartar wata Sallah da jagoran Kwankwasiyya tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi, wadda aka gudanar a filin kofar Na’isa, inda Babban Limamin Masallacin kofar Nasarawa Dokta Sani Ashir ya jagoranci Sallar da yin huduba a kan hukuncin da za a yanke.
Ganin fuskar Kwankwaso a wajen wannan Sallah tare da Gwamnan Kano Abba Kabiru Yusuf ya nuna cewa lallai akwai kalubale mai girma dangane da shari’ar da ake yi, wannan ya sanya tun a lokacin wasu masu nazari suka fara bayyana alamun lallai hukuncin da za a yanke ba zai yi wa ’yan Kwankwasiyya dadi ba.
Abin ya sake ta’azzara mako guda kafin yanke hukuncin, inda Gwamna Abba Kabiru Yusuf ya kori Kwamashinansa na Harkar kasa da wani Mai ba shi shawara kan matasa da ake kira da Ogan boye.
Gwamnan ya sallame su daga mukamansu ne saboda kalaman da suka yi na tunzura jama’a da kuma yin barazana ga alkalan da ke shari’ar zaben.
Gwamnan bai yi wata-wata ba ya sallame su daga aiki, saboda kalaman da suka yi na cin zarafi da barazana ga alkalan da kuna Mataimakin Shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.
Ranar da aka yanke wannan hukunci, abin ya zo da ba-zata. Domin kuwa, alkalan da za su yanke hukunci game da zaben ba zu iya halartar zaman kotun ba, sai suka yi amfani da manhajar Intanet da ake kira Zoom ta yadda mutum zai yi magana ana kallonsa kuma ana jin sa, wannan abu ne da ba a saba ba, kuma hakan na nuna cewa barazanar da ’yan Kwankwasiyya suka yi gane da alkalan nan ya sanya ba za su iya halartar zaman kotun ba, sai dai su yi amfani da intanet, ta amfani da wannan hanyar ce dai aka yanke hukunci kan zaben Gwamnan.
Bayan daukar tsawon lokaci ana karanto hukuncin wannan kara, kotun ta tabbatar da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dokta Nasiru Yusufu Gawuna a matsayin wanda ya samu nasara a zaben da aka gabatar a watan Maris din da ya gabata.
Kotun ta zaftare kuri’u sama da dubu 100, wadanda aka tabbatar ba halattatun kuri’u ba ne, inda kuma bayan cire wadannan kuri’u, Dokta Nasiru Gawuna na Jam’iyyar APC ya kasance shi ne ke da nasara.
Magoya bayan Gawuna da suka yi cincirindo a Babban Masallacin Juma’a da ke cikin birnin Kano sun cika da sowa da murna bayan da gwaninsu ya samu nasara, yayin da magoya bayan Gwamna Abba Kabiru Yusuf wadanda ’yan Kwankwasiyya ne suka cika da bakin ciki da damuwa a wannan rana.
Sakamakon tsoron barkewar rikici ya sa Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24, kuma aka yi nasara babu wani abu na tashin hankali da ya biyo baya.
Sai dai kuma kamar yadda mutane ke cewa shari’a sabanin hankali, babu wanda yake da tabbas game da shari’ar har sai an saurari hukuncin karshe a Kotun Koli, domin kuwa idan muka kalli shari’ar zaben Gwamnan Jihar Osun, za mu ga cewar tsohon Gwamnan Jihar da aka kayar a zaben Gbenga Oyetola ya samu nasara a kotun farko da ta biyu, amma kuma da aka je Kotun koli sai ta sake tabbatar da Gwamna Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.
Wannan na nuna cewa komai na iya faruwa a Kotun Koli, Dokta Nasiru Gawuna na iya ci gaba da rike nasararsa har zuwa Kotun koli, kuma ana iya rusa hukuncin kotun farko da ta biyu kuma ana iya tabbatar da su duka. Don haka dai za mu ce wannan shari’a mace ce da ciki.
Bayan haka, akwai shari’un gwamnonin jihohin Kaduna da Sakkwato da Kebbi da Taraba da Nasarawa da Ogun wadanda dukkansu shari’o’i ne masu matukar daukar hankali.
Domin idan ba mu manta ba, kuri’u dubu 10 ne a kacal tsakanin Jam’iyyar PDP da APC a Jihar Kaduna, inda PDP din take zargin an yi arigizon kuri’u wadanda babu su a na’urar tantancewa ta BVAS. Ita ma shari’ar zaben Gwamnan Kaduna, mace ce da ciki komai na iya faruwa kamar yadda ya faru a Kano.
A Sakkwato kuwa, batu ne ake na takardun makaranta musamman a kan Mataimakin Gwamnan Jihar da ake cewa ba ya da sahihan takardun makarantar firame da kuma batun tafka magudi da ake zargin Jam’iyyar APC a jihar da aikatawa a yayin zaben.
Haka nan, a Jihar Nasarawa, tsakanin Jam’iyyar PDP da APC taki ne kalilan wanda shi ma komai na iya faruwa dangane da hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben.
Jihar Taraba ma, akwai kyakkyawan zaton cewar hukuncin na iya ba da mamaki a tsakanin Jam’iyyar NNPP da Jam’iyyar PDP kamar yadda a Jihar Kebbi ma, Jam’iyyar PDP ke kalubalantar sakamakon zaben Gwamnan Jihar da APC ta yi nasara.
Bayan nan sai Jihar Ogun inda ake zargin Jam’iyyar APC da tafka kazamin magudi da ya bai wa Gwamnan Jihar damar tsallakewa da kyar.
Dama kuma a yankin Kudu maso Yamma, jihohin Ogun da Legas ne suka fi daukar hankali a shari’un da ake gudanarwa. Na Legas dai Gwamna Sanwo-Olu ya tsallake a kotun farko.