✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaɓen Gwamna: An yi garkuwa da wasu jami’an INEC a Bayelsa

INEC ta ce wannan lamari zai iya kawo cikas ga sahihin zaɓe.

Hukumar Zaɓe ta Kasa INEC ta ce an yi garkuwa da wasu jami’anta a Karamar Hukumar Brass ta Jihar Bayelsa yayin da ake ci gaba tattara sakamakon zaben gwamna.

Sanarwar da INEC ɗin ta wallafa a shafinta na dandalin X na zuwa ne kwana ɗaya bayan sakin Baturiyar Zaɓe, Ebehireme Blessing Ekwe, wadda aka yi garkuwa da ita a jihar ta Bayelsa kafin fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamna na ranar Asabar.

A cewarta, “wannan lamari zai iya kawo cikas ga sahihin zaɓe.”

INEC ta ƙara da cewa, “muna kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kuɓutar da su.”

Aminiya ta ruwaito yadda ’yan siyasa suka rika sayen kuri’un masu zabe kan N12,000 zuwa N40,000 a zaben Gwamnan Jihar Bayelsa.

Dan takarar Jam’iyyar LP, Udengs Eradiri, ya bayyana damuwa bisa da yadda matsalar sayen kuri’u ta yi muni a zaben da aka gudanar ranar Asabar.

Da yake jawabi a yankin Agudama-Ekpetiama bayan kada kuri’arsa, Eradiri ya ce shi kansa masu zabe sun tunkare shi suna neman ya sayi kuri’arsu, amma ya ki amincewa.

“Abin da ya fi ba ni takaici shi ne yadda wata mata da na dauki nauyin karatun danta, ta sayar da kuri’arta a kan N14,000,” in ji shi.