✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta tashi a Kasuwar Gamboru da ke Maiduguri

Babbar Kasuwar Gamboru ta yi gobara bayan wata biyar da wata gobara ta lakume bangaren kasuwar

Gobara ta tashi da tsakar dare a Babbar Kasuwar Gamboru da ke Maiduguri a Jihar Borno.

A safiyar Lahadi gobarar ta tashi, wata biyar makamanciyarta ta cinye wani bangare na kasuwar.

Zuwa lokacin da wakilinmu ya turo mana rahoto, gobarar tana nan tana ci.

Wasu shaidu a kasuwar sun shaida wa wakilinmu cewa wutar ta fara ci ne da tsakar dare daga ɓangaren masu sayar da kayan miya.

Zuwa wannan lokaci dai ba a kai ga gano asalin abin da ya haddasa gobarar ba.

Amma an girke jami’an tsaro domin dakile ayyukan bata-gari.