✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zaɓen 2027: Babu ɗan takarar da zai yi nasara ba tare da goyon bayan Arewa ba — Hakeem

Mun dawo daga rakiyar yaudarar da ake yi mana ta zaɓen ɗan takara saboda ƙabilanci ko addini.

Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba.

Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf.

Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa.

“Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa mutanen sauran yankunan ƙasar.

“Sai dai abin da muka sani ƙarara shi ne babu wanda zai zama shugaban Nijeriya ba tare da goyon bayan Arewa ba.

Ya bayyana damuwa kan yanayin da aka tsinci kai a ƙasar a halin yanzu, inda ya buƙaci ’yan Arewa da su guji faɗa wa tarkon ’yan siyasa mayaudara a zaɓen da ke tafe.

“Muna so a samu gwamnatin da ta fahimci matsalolinmu kuma wadda za ta iya magance su.

“Bayan shekaru takwas da Buhari ya yi a karagar mulki mun ƙara buɗe ido. A yanzu wata gwamnatin ce amma har yanzu kuka muke yi. Shikenan kullum a kuka za mu ƙare?

Kazalika, Baba-Ahmed ya bayyana yadda yankin Arewa ya tagayyara a sakamakon rikicin Boko Haram wanda ya taɓa duk mabiya addinai, lamarin da ya jaddada muhimmancin haɗin kai.

“Mun dawo daga rakiyar yaudarar da ake yi mana ta zaɓen ɗan takara saboda ƙabilanci ko addini. Yanzu an rufe wannan babi.

“Yanzu abin da kawai muke buƙata shi ne shugaba nagari wanda zai magance matsalolin da muke fama da su,” in ji shi.