✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yusuf Falgore ya zama sabon Shugaban Majalisar Kano

Muhammad Bello Butu-Butu ya zama mataimakin Falgore.

An zabi wakilin Karamar Hukumar Rogo, Yusuf Ismail Falgore a matsayin sabon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Haka kuma, an zabi wakilin Rimin Gado da Tofa Muhammad Bello Butu-Butu a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.

Wadannan sabbin shugabanni dai su ne za su maye gurbin tsoffin shugabannin majalisa ta 9, wato Hamisu Chidari da kuma Kabiru Hassan Dashi.

Aminiya ta ruwaito cewa, a wannan Talatar ce ake zaben shugannin majalisu a jihohi daban-daban da kuma a matakin tarayya.