✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yusuf Dingyadi: Magayakin Garkuwan Daular Usmaniyya

A ranar Asabar da ta gataba ce aka nada Bagizage Yusuf Abubakar Dingyadi (08035877331) sarautar ‘Magayakin Garkuwan Sakkwato.’ A yayin dabdalar cin abincin dare da…

A ranar Asabar da ta gataba ce aka nada Bagizage Yusuf Abubakar Dingyadi (08035877331) sarautar ‘Magayakin Garkuwan Sakkwato.’ A yayin dabdalar cin abincin dare da aka gabatar a ranar Juma’a, a otel din Pinnacle kuest Inn, Sakkwato, domin taya Magayakin murna, Farfesa Salisu Ahmad Yakasai na Jami’ar Usman danfodiyo Sakkwato ya gabatar da tsokaci na musamman game da rayuwarsa. Ga wani bangare na tsokacin kamar haka:
Ko shakka babu a duniyar aikin jarida, Yusuf Dingyadi ba ya bukatar gabatarwa. Kamar yadda ya shige gaba a fagen rubutu da marubuta, to ya kuma yi fice a haujin siyasar yau, a hobbasarsa ta ganin an samar da kyakkyawan shugabanci a Tarayyar Najeriya, musamman ma bayan gurbacewar lamura a tafin hannun Shugaba Goodluck Jonathan.
kwararre ne da gogewa cikin aikin da ya fi iyawa da lakanta. Hasali ma, shekaru da dama da suka wuce zuwa yanzu, wasu na ganin a aikin jarida dai, Dingyadi ya yi wa tsara ratar da sai dai su biyo sahu, domin ko ba komai carar da zakaransa ya yi, ta sa an jiyo amonsa a ko’ina. Wadanda suka san shi da wadanda suka kusance shi da kuma wadanda suka yi mu’amala da shi, sun bayyana shi a matsayin mutum mai jajircewa da naciya da sadaukar da kai, domin ganin an samu biyan bukatar da ake bukata, a lokacin da ake bukata ba tare da rashin biyan bukata ya rinjayi bukatar da ake bukata ba.
Haka ma shekarunsa na rayuwa, shekaru ne da ya rayu rayuwa tagari, rayuwa abar muradi kuma rayuwar Allah-sam-barka, cikin yadda aka shaide shi da biyayya ga magabata da mutunta tsara da kuma zama lafiya da matasa. A daya gefen, tare da kasancewa a bisa alkiblar da yake ganin ita ce mafi a’ala kuma mafi dacewa a gare shi da sauran al’umma, ba tare da kaucewa al’kiblar ba, duk kuwa da bukatar wasu ta son ganin ya kauce wa inda ya dosa.
Don haka jama’a da dama ba su yi mamaki ba, lokacin da Garkuwan Daular Usmaniyya, Dakta Attahiru dalhatu Usman Bafarawa ya aminta da nadin mashawarcinsa ta fuskar aikin jarida a matsayin Magayakinsa, wato Magayakin Garkuwa, wanda zai shige kan gaba wajen kariyar kowace irin arangama da artabun da aka kai ko ake shirin kai wa Garkuwa a fagen fama. Haka kuma, shi ne zai zamo Magayakinsa ta fuskar rungumar kowace irin kwaramniyar murhun siyasa a yau da gobe. Bugu da kari, shi ne Magayakinsa a aikin jarida. Shi kuma Garkuwa, zai ci gaba da aikinsa na kariyar katafariyar Masarautar Daular Usmaniyya.
Tarihi ya bayyana cewa, marigayi Mai Martaba Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido (Allah Ya lullube shi da RahamarSa) shi ne ya nada Attahiru Bafarawa a bisa sarautar Garkuwan Daular Usmaniyya a farko-farkon hawansa kan karaga. Shi kuma daga baya ya nada wasu mutanensa a sarautu daban-daban.
Haduwa Da Bafarawa: A tattaunawar musamman da ya yi da wannan marubucin, Dingyadi ya bayyana cewar, duk wanda ya kwana ya tashi a kasar nan ya san da zaman Bafarawa, amma fa bai samu sa’ar fara hulda da shi ba sai a 1987, a lokacin da Bafarawa ya kara yin fice wajen taimaka wa al’umma, musamman a kungiyance lokacin da yake jagorantar Bafarawa Social Club. dan jaridar ya ce: “Mun shaku da Bafarawa sosai a 1993, hasali ma daga lokacin har zuwa lokacin dawowar mulkin siyasa muna tare, duk da cewa ba mu taba siyasa tare ba sai a 2007.” Ya kara da cewar: “Ina matukar farin ciki sosai da a yau Garkuwa ya ba ni wannan sarautar ta Magayakinsa.”
kima Da Tasirin Bafarawa: Magayakin Garkuwa ya bayyana Bafarawa a matsayin nagartaccen basarake kuma dan gwagwarmayar siyasar ci gaban al’umma, wanda a jiya da yau hidimar al’umma ya sa a gaba. Ya kuma ce Garkuwan Sakkwato “Dattijo ne a magana, kuma dattijo ne a kowane irin lamari, domin a bayyane take bai taba sa kansa a kowane irin lamari na ba daidai ba. A lura Garkuwa ba ya sa kansa a lamarin sabon Allah kuma ba ya sa kansa a wajen cutar jama’a, illa iyaka yakan sa kansa a duk wata harka da za ta amfani jama’a. Kazalika, mutum ne wanda ya san daraja da ciwon wadanda yake tare da su. Baya ga wannan, mutum ne mai son aiwatar da gaskiya tare da taimakon marasa gata.”
Ayyuka Da Tattaki A Cikin Tarihi: Tattaki a cikin tarihi, za a ga Yusuf Abubakar Dingyadi ya zo duniya shekaru arba’in da suka gabata a garin Kwalfa da ke Gundumar Dingyadi, a karamar Hukumar Bodinga. Bayan karatun addinin Musulunci a shekarunsa na farko, ya kuma samu kansa a karatun boko domin samun gishirin zaman duniya, ta yadda a yau yake da muhimman takardun shaidar samun ilimi tare da shugabancin kamfanin tuntubar aikin jarida na Dingyadi Media Serbices a matsayin babban jami’in gudanarwa.
Bisa ga sha’awar da yake da ita ta aikin yada labarai, Dingyadi ya fara aikin jarida da Mujallar Zuma mallakar Umaru Dembo a 1991. Ya kuma yi aiki da Mujallar Nasiha daga 1992-1993,  daga baya kuma ya rika aikawa da labarai a Mujallar Sentinel a Kaduna, gabanin ya samu aiki da Democrat.
Likkafar Dingyadi ta yi gaba a yayin da Sashen Hausa na gidan Rediyon BBC ya yaba wa jajircewa da gogewarsa, wadda ta zama silar daukarsa aiki a BBC a shekarar 1994, a matsayin wakilin gidan rediyon da ke aika labarai daga tsohuwar Jihar Sakkwato da Kebbi da Katsina da kuma wani bangare na Jamhuriyar Nijar.
Bayan barin BBC Hausa, Dingyadi ya zama karamin Daraktan yada labarai na yakin neman zaben Obasanjo da Atiku a 1999. Bayan samun nasarar lashe zabe, ya zama mataimaki na musamman ga Ministan Sadarwa, Alhaji Arzika Tambuwal, kamar dai yadda ya zama mataimaki na musamman ga Jakada Ladan Abdullahi Shuni a matsayin mai kula da kididdigar ’yan Nijeriya da ke shiga birnin Casablanca daga kasar Morocco. Ya kuma yi aiki a matsayin mataimaki na musamman kan aikin jarida ga marigayi Garba Koko, Sarkin Yakin Gwandu a lokacin da yake a matsayin Shugaban Jam’iyyar SDP da kuma lokacin da yake a matsayin shugaban makarantar horar da ma’aikata (ASCON) da ke Lagos.

HIDINDIMUN GIZAGAWA

Gizagawan Jihar Kaduna za su gudanar da taronsu a jibi Lahadi da misalin karfe 11:00 na safe, a ’Yankeke PZ, Zariya. Domin karin bayani sai a tuntubi PRO Tukur Abdullahi Kudan (08036003631).
***
A labarin jajantawa kuwa, Muhammad Yusuf ’Yandoma 08039355855, mahaifinsa, Alhaji Muhamad Sada Maifata ’Yandoma ne Allah Ya yi wa rasuwa a Lahadin da ta gabata.
Muna rokon Allah Ya jikansa da rahama, Ya ba iyalansa hakuri. Mu kuma da muka rage, Allah Ya ba mu ikon cikawa da ingantaccen imani, idan tamu ta zo. – Gizago!
***
A wannan makon, ga Gizagawan da suka samu rijista:
1-Bello Hussaini Muhammad Kazaure, 08060602370 (GZG606JGW). 2-Nazifi Muhammad Baura Kazaure, 07062555586 (GZG607JGW). 3-Sulaiman Muhammad, 08098064813 (GZG608FTK). 4-Usman Ibn Hassan Gombe, 08035545909 (GZG609GMB). 5-Alhaji danladi kofa, 07035699758 (GZG610LGS). Musa Umar Muhammad Bauchi, 08189258383 (GZG611BAU).