✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yunwa ce ta sa mu yin fashi da makami’

Wasu matasa da aka kama da zargin fashi sun ce ‘yunwa da suka fuskanta a lokacin dokar kulle ce ta sa suka fara yin fashi.…

Wasu matasa da aka kama da zargin fashi sun ce ‘yunwa da suka fuskanta a lokacin dokar kulle ce ta sa suka fara yin fashi.

Wani dan shekara 25 mawakin hip-hop mai tasowa da abokinsa makadi mai shekara 22, na daga cikin gungun mutum shida da aka kama ranar Laraba, a samamen da ‘yan sanda suka kai a wani rukunin gidaje a Ajah, jihar Legas.

“Kusan mako biyu ba mu da abin da za mu ci a lokacin dokar kulle. Masu shaguna na bin mu kudi, ba mai son ba mu bashi. Dole muka nemi yadda za mu rayu a cikin kullen”, a cewar wadanda ake zargin.

Sama da makonni goma ke nan da Gwamantin Tarayya ta fara sanya dokar kulle kafin a sassauta ta a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja saboda dakile yaduwar cutar coronavirus.

Abin da ya faru

Matashin mawakin ya yi odar wayar iPhone Max Pro daga shagon intanet na jiji.com a kan Naira 450,000, cewa zai biya kudin idan aka kawo, inji ‘yan sanda.

Bayan an kawo wayar sai ya tura wa dan aiken kamfanin sakon biyan kudin na bogi, sannan ya hada baki da makadin suka daure dan aiken suka tsere.

Daga baya sun sayar da wayar a Ikeje a kan Naira 350,000 wanda kuma aka tura wa shi mawakin ta banki.

‘Yan sandan sun ce wadanda ake zargin sun shaida musu cewa sau uku suna sayar da irin wayar a cikin dokar kullen. Sauran wayoyin biyu sun saye su ne da katin kudi da suka sace wa wasu.

Yadda aka kama su

Wakilinmu ya ce an kama mawakin ne tsirara a kan titi bayan ya duro daga bene, a kokarinsa na guje wa ‘yan sanda. Daga nan aka wuce da shi asibiti sakamakon kujewar da ya yi a fuskarsa.

‘Yan sanda sun ce matasan sun shaida musu cewa suna yin wasa akai-akai a wasu gidajen casu a Legas.

Sun ce wadanda ake zargin sun dora laifin abin da suka yi a kan yunwa sakamakon dokar hana fita domin kauce wa yaduwar cutar COVDI-19.

“Kusan mako biyu babu abin da za mu ci a lokacin dokar kulle. Masu shaguna na bin mu kudi, ba mai son ba mu bashi. Dole muka nemi yadda za mu rayu a cikin kullen”, a cewar wadanda ake zargin.

Suna taba harkar ‘yahoo’

Abubuwan da aka gano daga hannun matasan wadanda suka ce bayan harkar waka, suna yin damfara ta intanet, sun hadar da manyan wayoyi uku samfurin iPhone da Samsung, kwamfutoci uku da sauran kayan hadawa da kuma shiga intanet.

‘Da yake bayani a kan kamen, Kwamishina ‘Yan Sanda na jihar Legas, Hakeem Odumosu,  ya ce duk da cewa intanet na samar wa jama’a damar cimma burinsu, rundunar ba za ta bari miyagu su yi amfani da shi wurin cutar da masu halastattun harkoki ba.