Shahararren ɗan daudun nan Bobrisky ya tabbatar wa wata Babbar Kotun Tarayya da ke Legas cewa shi namiji ne kawai shigar mata yake yi.
Bobrisky ya shahara wurin shigar mata, har ta kai ga a kwanakin baya aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe gasar kwalliya a tsakanin mata.
Ya jima yana jan zarensa a kafafen sada zumunta a matsayin namijin da ya koma mace, har cewa yake yana ganin jinin al’ada ko kuma yana ciwon ciki kafin zuwan al’adarsa.
Mai Shari’a Abimbola Awogboro ya tambayi Bobrisky “kai namiji ne ko mace?”
Sai Bobrisky ya kada baki ya ce “Ni na miji ne ya mai shari’a.”
Bayan wannan takaddamar ce dai mai shari’ar ya yanke wa Bobrisky hukuncin zaman gidan yari na watanni shida.
An dai kama Bobrisky ne a ranar 24 ga Maris, kuma aka gurfanar da shi a gaban kuliya bayan ya amsa laifinsa na wulakanta takardun Naira ranar 5 ga Afrilu.
Alƙalin ya ce, zaman gidan yarin Bobrisky zai fara ne daga ranar 24 ga Maris, 2024, wato ranar da aka kama shi a karon farko.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC dai ce ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume shida.
An yi watsi da tuhume-tuhume biyu, yayin da ya amsa laifin cin zarafin Naira, amma ya nemi a yi masa afuwa a matsayinsa na wanda ya fara aikata laifi.
EFCC ta soma gayyatar Bobrisky ne bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda mai shekara 31 a duniyar ke yin liƙi da sabbin banduran takardun naira.
Hukumar ta ce bidiyon ya naɗo Bobrisky yana watsi da takardun kuɗin a bikin nuna wani fim mai suna Ajakaju wanda jarumar Nollywood, Eniola Ajao ta shirya da aka yi ranar 24 ga watan Maris a shagon Film One Circle Mall da ke Lekki a Jihar Legas.
EFCC ta ce a baya ma an samu Bobrisky da aikata laifin da ake zargi a wasu tarukan sharholiya, kamar yadda EFCC ta ce bincike ya nuna.