Mahautan Babbar Kasuwar Shanu ta Abbatuwa da ke Legas sun yi sabon Sarkin Fawa bayan shafe shekara 20 da rasuwar Sarkin Fawa Alhaji Ɗan’azumi, wanda lamarin da ya zo musu da farin ciki da fatan alheri.
Naɗin sabon Sarkin Fawan Abbatuwa, Alhaji Bala Umaru wanda aka fi sani da Bala Katako, ya zo ne bayan da mahautan Kasuwar Abbatuwa suka ziyarci gidan Sarkin Fulanin Legas, Alhaji Muhammadu Abubakar Bambaɗo, inda suka kai masa ziyarar gaisuwar Sallah.
- Yadda Adam Zango ya girgiza teburin Kannywood
- Iyayen matashi sun buƙaci ’yan sanda su tuhumi wata kan mutuwar ɗansu
Mahautan sun kuma miƙa masa takardar buƙatarsu suna roƙon ya taimaka ya naɗa masu Sarkin Fawan Kasuwar Abbatuwa duba da tsawon shekaru da suka yi babu Sarkin Fawa a kasuwar duk da irin muhimmancinta a harkar fawa a Legas.
Bayan da Sarkin ya ji koken nasu ne, suka gabatar masa da sabon Sarkin shi kuma ya amince kasancewarsa sanannen mutum ne, mai biyayya, mai taimako, wanda ya shafe shekaru da dama yana bauta wa jama’a a Kasuwar Abbatuwa, don haka nan take ya ba da umarnin a naɗa shi sarautar Sarkin Fawa kamar yadda suka buƙata.
Daga bisani ya yi kira ga ɗaukacin jama’ar kasuwar su yi masa mubaya’a da biyayya, yayin da ya yi kira ga Sarkin Fawan Abbatuwar, ya gudanar da shugabancinsa cikin adalci, tare da ɗaukar shawarar dattawa.
A hirar Aminiya da sabon Sarkin Fawan bayan ya yi wa Allah godiya, ya ce, mahautan kasuwar sun daɗe suna yi masa tayin sarautar Sarkin Fawa, sai daga baya ya dubi masalahar ci-gaban masu sana’ar a kasuwar musamman ma matasa ya amince.
Ya ce zai yi tabbatar da haɗin kai da ci-gaban mahauta da sana’ar fawa da ɗaukacin ’yan Kasuwar Abbatuwa da jihar baki ɗaya kasancewar a cikin sana’ar aka haifi iyaye da kakanninsa.
“Wannan sana’a cikinta na taso kuma zan yi duk abin da zan iya don ci-gabanta musamman a Kasuwar Abbatuwa, don haka ina neman goyon bayan al’ummarmu, masu ƙauna da masu adawa kowa a yanzu nawa ne,” in ji shi.
Da ya ke tofa albarkacin bakinsa a kan naɗin Sarkin Fawan, Sarkin Fulani Kasuwar Alhaji Bello Ɗan Mubaffa, ya ce, ce sun yi farin ciki sosai duba da ci gaba da mahautan kasuwar suka samu na samun jagora.
“Kuma jagoran ma jajirtacce wanda yaronmu ne a nan muke tare da shi sama da shekara 40, ba mu taɓa samunsa da wani abin ƙi ba.
“Fatana yadda mahauta suka nuna masa goyon baya, to su ci-gaba da jajircewa a bayansa,” in ji shi.
Naɗin na Alhaji Bala ya kawo ƙarshen rigingimu da abubuwa masu kama da haka waɗanda su ne a baya suka gurgunta sarautar Sarkin Fawa a Kasuwar Abbatuwa suka sa aka gaza samun sabo, a cewar Shamsudeen Lawal, wani matashin mahauci a kasuwar.