✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yunwa ba za ta sa mu janye yajin aiki ba — ASUU

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta ce Gwamnatin Tarayya ba za ta yi nasara ba kan yunkurin da take na amfani da yunwa wajen…

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta ce Gwamnatin Tarayya ba za ta yi nasara ba kan yunkurin da take na amfani da yunwa wajen tilasta wa mambobinta komawa aji.

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels ya yi da shi a ranar Laraba.

Osadeke ya ce Gwamnati ta hana su albashinsu tun bayan da suka soma yajin aiki a watan Fabrairun da ya gabata.

“An rike mana albashinmu. Muna cikin wata na shida ke nan rabonmu da albashi,” inji shi.

Ya kara da cewa, “A zatonsu, idan suka hana mu albashi na wata biyu ko uku, za mu roke su a kan su kyale mu, mu koma bakin aiki.

“Amma a matsayin kungiya ta masana, matsayinmu ya wuce haka. Ba zai yiwu a yi amfani da yunwa wajen mayar da mambobinmu bakin aiki ba, wanda hakan shi ne abin da gwamnati ke kokarin aiwatarwa.”

ASUU ta tsunduma yajin aiki ne domin neman hakkokinta daga wajen gwamnati da suka hada da neman aiwatar da yarjejeniyarsu da gwamnati ta 2009, amfani da tsarin UTAS wajen biyan albashi da sauransu.

A ranar Litinin din da ta gabata ce ASUU ta tsawaita yajin aikin nata da karin wasu makonni hudu don bai wa gwamnati isasshen lokaci wajen cim ma bukatunta.

%d bloggers like this: