✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunkurin yajin aikin kungiyar NUPENG

A ranar 30 ga Mayu, 2014 kungiyar kananan ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Najeriya (NUPENG) ta ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 14 don shawo…

A ranar 30 ga Mayu, 2014 kungiyar kananan ma’aikatan Man Fetur da Gas ta Najeriya (NUPENG) ta ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 14 don shawo kan rikicin da ya dabaibaye kungiyar Masu Kasuwancin Man Fetur ta Najeriya (IPMAN). Tabbas wannan yunkurin zai rattaba tsoron karancin mai a zukatan jama’a. Shugaban NUPENG Igwe Achese ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa manema labarai karin bayani a Legas, inda ya ce rikicin da ya dabaibaye IPMAN na daya daga cikin manyan dalilan da ya sa suka ba Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 14.
Ya ce idan har gwamnati ta kasa shawo kan matsalar a zuwa ranar Alhamis (jiya), to babu makawa zai hada kan ’yan kungiyarsu don fara yajin aiki. Don ya tabbatar da gaske yake sai ya bukaci Babban Mai Shari’a na Najeriya kuma Babban Atoni na Gwamnatin Tarayya da ya shawo kan matsalar.
Abin takaici ne a ce don akwai matsalar shugabanci a kungiyar IPMAN sai a yi barazana yajin aiki don tilasta wa kotu ta  yanke hukunci cikin gaggawa ba tare da an bi ka’idar shari’a da kuma abin da ya dace ba.
Yin barazanar yajin aikin shisshigi ne ga harkokin shari’a, kuma abin damuwa da allawadai ne.
Yajin aiki sahihin mataki ne da Hukumomin kwadago za su iya amfani da shi wajen nuna abin da aka yi musu ba daidai ba har a samu maslaha. Idan aka yi la’akari da yadda yajin aiki ya nakasa abubuwa a kasar nan, bai kamata a rika yi wa batun yajin aiki daukar sako-sako ba. Tun ba a je ko’ina ba tuni kalaman Achese suka haifar da dogayen layuka a gidajen mayukan da ke wadansu garuruwan kasar nan.
Babban dalilin da ya sa NUPENG ke barazanar yajin aikin shi ne, rikicin shugabancin da yake addabar kungiyar IPMAN bayan an kammala zaben shugabannin kungiyar.
A cewar wasu NUPENG ta yi yunkurin yajin aikin ne sakamakon hasashin da aka yi cewa tuni bangaren shari’a ya goyi bayan wani bangaren masu rikicin. Yajin aikin ba zai haifar wa mulkin dimokuradiyya da aka shafe 15 ana yi a kasar nan da mai ido ba. Ba zai taba kare kundin tsarin mulkin kasar nan ta kowane bangare ba, musamman ma da a yanzu duniya ta zuba wa kasar nan idanu ba.
Ya fitar da wannan sanarwar ne sakamakon hukuncin biyu da wadansu kotuna biyu suka yanke kan rikicin shugabancin IPMAN din. Na farko a Fatakwal; na biyu kuma a Abuja. Babbar Kotun Fatakwal ta yanke hukuncin da ya hana wani mutum mai suna Mista Obasi Lawson, (wanda alama ta nuna Achese yana goyon bayansa) zama shugaban kungiyar IPMAN na kasa. A zaman Babbar Kotun Abuja kuma ta yanke hukuncin da ke haramta sababbin shugannin kungiyar. Don haka ne ’yan kungiya za su iya amfani da dukkan hukuncin da suka fi so, kamar yadda kundin tsari ya amince da hakan, amma batun yin barazanar yajin aiki don tilasta wa kotu ta yanke hukuncin da zai amfani su Achese ya yi tsanani. Akwai hanyoyin da zai bi don a saurare shi, amma ba wai ya kira taron manema labarai sannan ya yi barazanar yajin aiki ba, wannan hanyar ba ta ciki kuma ta yi muni.
Bai kamata a rika bakanta gwamnati ko jami’anta ko hukumominta don kawai cim ma biyan bukatar kashin-kai ba duk da cewa shari’ar tana gaban kotu ba.
Yunkurin yajin aikin da NUPENG za ta yi, wata hanya ce ta cutar da al’umma don kawai a cim ma biyan bukatar kai. Kada a bari hakan ya kasance.
Muna kira ga mambobin NUPENG kada su bari a yi amfani da su don biyan bukatar wadansu, su fahimci hakan zai cutar da al’umma.