✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yunkurin sayen kuri’u: An kama dan majalisa da tsabar $498,100 a Ribas

An kama shi ne ana jajiberin zabe

’Yan sanda a Jihar Ribas sun cafke dan Majalisa Wakilai mai wakilatar mazabar Fatakwal II, Chinyere Igwe, da tsabar kudi har Dalar Amurka 498,100, ana jajiberin zabe.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Grace Iringe Koko ta fitar, ta tabbatar da kama dan majalisar, wanda dan jam’iyyar PDP ne da yake neman a sake zabensa.

Kazalika, ’yan sandan sun kuma ce sun kama shi da jerin sunayen mutanen da yake shirin raba wa kudin, da nufin sayen kuri’a.

Ta ce tuni Mataimakin Sufeto-Janar (AIG) mai kula da harkokin zabe a Jihar, Abutu Yaro, ya bayar da umarnin zurfafa bincike domin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.

Ya kuma bukaci dukkan ’yan takara da jam’iyyun siyasa da su bi dokokin zabe sau da kafa, tare da neman jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro bayanan sirrin da za su kai ga kama bata-gari.

Kamun dan majalisar dai na zuwa ne kwana biyu bayan wata kotun majistare da ke zamanta a Fatakwal ta aike da dan majalisa mai wakiltar mazabar Etche/Omuma a Majalisar Wakilai, Ephraim Nwuzi, gidan yari.

An dai yanke Ephraim, wanda dan jam’iyyar APC ne hukuncin bayan ’yan sanda sun zarge shi da tayar da rikicin kabilanci a tsakanin jama’a.