Majalisar Tarayya ta ce ’yan Najeriya su daina yi mata shagube kan yoyon da rufin gininta ya yi sakamakon ruwan sama.
Ruwa ya malale cikin ginin Majalisar sakamkon yoyon rufin ginin a lokacin da aka tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a Abuja ranar Talata.
- ’Yan fashi sun yi hatsari a hanyarsu ta tserewa
- Maganin gargajiya ya yi ajalin mutum 10 ’yan gida daya
Bidiyon lamarin ya nuna yadda ma’aikatan Majalisar suka fito da injina da sauran kayan shara suna ta fadi tsahin kwashe ruwan da ke ta malala.
Hakan ya jawo caccaka musamman daga kungiyoyin fararen hula da na kare hakki, inda suka bayyana shi a matsayin babban abin kunya ga kasa.
Majalisar ta kuma sha zargi daga wasu ’yan Najeriya cewa duk da Naira biliyan 37 da aka ware domin gyaran ginin Majalisar, sai ga shi rufin ginin yana yoyo.
Amma Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce ginin Majalisar ya dade yana bukatar gyara, don haka ba abun mamaki ba ne don kwanon ya fara yoyon ruwan sama.
Lawan ya ce yoyon rufin ya tabbatar da gaskiyar matsayin ’yan majalisar tun ba yanzu ba na cewa ginin na bukatar gyara.
“A ganina yoyon shaida ce da ke tabbatarwa tare da wanke Majalisar game da matsayin da ta dauka a baya.
“Sanin kowa ne cewa tun ba yau ba wurin nan na bukatar gyara. Mun je mun ga Shugaban Kasa, kuma ya amince, ya sa in tattauna da hukumar FCTA, wadanda su ke da ginin.
“Ni da Shugaban Majalisar Wakilai da tsohon Shugaban Ma’aiaktan Fadar Shugaban Kasa (marigayi Abba Kyari), da Ministar Kudi mun tattauna kan yadda za a samu kudin gyaran.
“Ko da aka amince da Naira biliyan 37 din, ba kasafin Majalisar Tarayya ba ce, kasafin FCDA ne.
“Idan wurin na yoyo, ya nuna ba mu ba dimokuradiyyarmu da muimmancin da ya dace ba; Saboda haka mun yi zaton kafafen yada labarai za su sanar da mutane tare da nuna sanin ya kamata.
“Wannan gurin na ’yan Najeriya ne kuma yana bukatar gyara.”