✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yin karin albashin ma’aikata zai haifar da matsala —Gwamnati

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ce ya kamata a yi wa ma'aikata karin albashi

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta jaddada bukatar a yi wa ma’aiaktan gwamnati karin albashi da alawus-alawsu dinsu.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya, Ayuba Wabba, shi ne ya yi kiran a lokacin taron tattaunawa tsakanin kungiya da bangaren Gwamnatin Tarayya wanda Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Folasade Yemi-Esan ta jagoranta.

Wabba wanda ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan aiwatar da mafi karancin albashin N30,000, ya kara da cewa, “Matsalar karancin albashi abu ne da ya shafi kowane bangare na ma’aikata.”

Ya ce, “A aikin gwamnati mafi karancin albashi da kuma karin albashi ba abu daya ba ne.

“Ma’aikatan gwamnati da suke aiki a ma’aikatu, musamman ainihin ma’aikatu da hukumomi su ne masu albashin da bai taka kara ya karya ba.

“Saboda haka ya kamata su ma a kara musu kwarin gwiwa domin su ne ainihin masu gudanar da ayyuka da shirye-shirye da kuma tsare-tsaren gwamnati.”

Matsala za ta biyo baya

Sai dai, da take nata jawabin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayyar ta ce, yin karin albashin na iya haifar da nakasu.

Ta ambato Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, yana jaddawa a lokacin wani zama da suka yi  cewa, “A sanya sharadi cewa muddin muka kara wa ma’aikatan gwamnati albashi, to ya ya zama jazaman su rika yin duk ayyukan da suka rataya a wuyansu.

“Dalili shi ne za a rika hukunta duk wanda bai yi aikinsa ba, saboda haka ya kamata a famihci wannan,” inji ta.

Ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin daidaita albashin ma’aikatan gwamnati da masu rike da mukaman siyasa.

A cewarta, kwamitin zai kuma auna albashin ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, domin tabbatar da ba a yi wa ma’aikatan gwamnati kwange wurin biyan su albashi da sauran hakkokinsu.