Shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Akinwumi Adeshina, ya ce irin matakan da hukumomin Najeriya ke ɗauka a kan matatar Dangote na ɓata sunan ƙasar nan a idon masu zuba jari.
Yayin da yake mayar da martani a kan taƙƙadamar da ta kaure tsakanin Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) da kuma Dangote, Adeshina ya buƙaci taka-tsan-tsan saboda gagarumar rawar da Dangote ke takawa wajen buƙasa tattalin arziƙin Najeriya.
- Waɗanda suka yi zanga-zanga a 2012 na son danne haƙƙin jama’a — Atiku
- Ina roƙon ’yan Najeriya kada su yi zanga-zanga — Tinubu
Shugaban bankin, ya ce babu wani mai zuba jarin da zai sanya Dala biliyan 19 sannan ya zuba ido yana kallon masu shigar da mai ƙasar suna masa zagon ƙasa.
Adeshina, ya koka kan yadda ake samun sauye-sauye a manufofin Gwamnatin Tarayya wadanda ke yi wa harkokin kasuwanci illa.
A saƙon da ya wallafa, wanda Femi Otedola ya yaɗa ta kafar X, ya ƙara da cewar sarrafa kayayyaki a Najeriya na da matuƙar wahala saboda irin ƙalubalen da ake fuskanta waɗanda suka haɗa da rashin sahihancin manufofin gwamnati, abin da ke bayar da damar mayar da hankali wajen shigar da kayayyakin da aka sarrafa daga ƙasashen waje.
Dangane da zargin da ake yi wa kamfanin Dangote na ƙin ganin abokan fafatawa a harkokin kasuwanci, Adeshina ya ce Dangote bai hana wasu kafa matata irin ta shi ba.
Har wa yau, yce kuskure ne a ce Dangote zai dinga fafatawa da masu shigar da mai daga ƙasashen waje, saboda haka adalci shi ne waɗannan mutane su kafa matata a Najeriya kamar yadda ya yi.
Adeshina, ya ce kuskure ne babba a yi wa kamfanonin cikin gida zagon ƙasa, ko kuma a masa tarnaƙi wajen gudanar da harkokinsa ta yadda zai durƙushe.