Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero da dan takarar Gwaman Jihar na Jam’iyyar APC Malam Nasir El-Rufa’i da Sheikh Ahmad Gumi na daga cikin daruruwan mutanen da suka halarci jana’izar Sheikh Muhammad Bello Al’adamawi wanda ya rasu a daren Litinin da ta wuce a Kaduna. Sheikh Al’adamawi wanda sananne ne a wajen yin wa’azin Musulunci a jihar ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya a gidansa da ke Hayin Malam Bello, Rigasa. Sheikh Muhammad Bin Usman Kano ne ya sallaci gawar marigayin da misalin karfe 11:00 na rana a gidansa. Kuma Gwamna Ramalan Yero da Malam Nasir El-Rufa’i duk sun samu sallar gawar tare da dimbin jama’a. Sauran malaman da suka halarci jana’izar sun hada da Shugaban Majalisar Malamai da Limamai ta Jihar Kaduna, Sheikh Abubakar Babantune da Sheikh Muhammad da Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun da Sheikh Umar Shehu Zariya da Babban Limamin Masallacin Juma’a da ke titin Nnamdi Azikwe a Tudun Wada, Ustaz Khamis Al-Misiri da Ustaz Musa Asadus Sunnah da sauran malamai. Marigayi Al-Adamawi ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya an kuma binne shi ne a makabartar Rigasa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Yero da El-Rufa’i sun halaraci jana’izar Sheikh Al’adamawi
Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero da dan takarar Gwaman Jihar na Jam’iyyar APC Malam Nasir El-Rufa’i da Sheikh Ahmad Gumi na daga cikin…