✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yayin da mahaifin Alampasu ya yi murnar rabuwa da acaba

Nasarar da Golan Najeriya Dele Alampasu ya samu a gasar cin kofin duniya na matasa da aka kammala a Dubai a shekarar  bara ta sa…

Nasarar da Golan Najeriya Dele Alampasu ya samu a gasar cin kofin duniya na matasa da aka kammala a Dubai a shekarar  bara ta sa mahaifinsa ya daina sana’ar acaba a kauyensu, kamar yadda mahaifin Mista Tomi Alampasu ya bayyana wa‘yan jarida a karshen makon jiya.
Mahaifin Alampasu wanda a da ba shi da wata sana’a da ta wuce daukar fasinja a babur da aka fi sani da acaba a kauyensu da ke Itoki a karamar Hukumar Ito da ke Jihar Ogun ya ce tun bayan da ’yan kwallon U-17 Golden Eaglets na Najeriya suka lashe kofin duniya a bara ciki har da dansa Dele, rayuwa ta canza masa don yanzu haka sai da ya wanke goma ya tsoma biyar don Allah Ya hore wa dansa dukiyar da za su cigaba da rayuwa daidai gwargwado.
“Yanzu haka Dele ya yi min alkawarin mayar da ni garin Abuja don na ci gaba da zama da shi a katafaren gidan da ya saya kuma na yi murna da hakan don tuni na yanke kaunar ziyarar Abuja balle a ce zan zauna a can”, inji shi.
Mista Tomi ya ce abin da ya fi faranta masa rai shi ne yadda dansa Dele ya kutubar da shi daga sana’ar acaba don dama tilas ta sa yake yi saboda halin rayuwa.
Tuni kungiyoyin kwallon kafa da dama a Nahiyar Turai suke  zawarcin Dele Alampasu don ganin ya sanya musu hannu kamar wasu daga cikin takwarorinsa suka samu nasarar samun kulob a sassan duniya.