✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Yayin da dan kwallon Aljeriya Brahimi ya lashe Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC

dan kwallon Aljeriya Yacine Brahimi ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka na BCC a bana.  Ya shiga gaban golan Najeriya bincent Enyeama…

dan kwallon Aljeriya Yacine Brahimi ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka na BCC a bana.  Ya shiga gaban golan Najeriya bincent Enyeama da sauran ’yan kwallo uku da suka fafata a gasar.
dan shekara 24 ya samu wannan nasara ce bayan masoya kwallon kafa sun kada masa kuri’a a gasar.
Wannan shi ne karo na farko da wani dan kwallo da ya fito daga Aljeriya ya taba lashe gasar.
A lokacin da Brahimi yake hira da sashen wasanni na BBC ya ce “”Na yi matukar farin ciki da na kasance Gwarzon dan kwallon Afirka na BBC a bana, don haka na sadaukar da wannan nasara ga kasata Aljeriya da kuma masoyan da suka kada mini kuri’a”.
Kimanin kasashe 207 ne da Hukumar FIFA ta amince suka kada kuri’a inda Brahimi ya samu nasara a kan sauran da suka fafata da suka hada da golan Najeriya bincent Enyeama da dan kwallon Gabon Pierre Emerick Aubameyang da ’yan kwallon Kwaddebuwa biyu Yaya Toure  da kuma Gerbinho.
A duk shekara ce ake gudanar da gasar.