✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya’yan Jam’iyyar APC a Jigawa ku dinke barakarku

’Ya’yan Jam’iyyar APC a Jigawa ku dinke barakarku Editan Aminiya. Ka ba ni dama in yi tsokaci game da barakar jam’iyyar APC a Jihar Jigawa.…

’Ya’yan Jam’iyyar APC a Jigawa ku dinke barakarku

Editan Aminiya. Ka ba ni dama in yi tsokaci game da barakar jam’iyyar APC a Jihar Jigawa. Ganin Buzu a masallaci, ya isa Tunkiya wa‘azi“. Na shigo da wannan karin magana ne ba don komai ba, sai don in yi kira ga ‘yan jamiyyar APC a jiharmu Jigawa, da mu yi wa kanmu kiyamul-laili, wajen kauce wa bambancin da ke tsakaninmu, mu sanya jam’iyyarmu gaba, domin bai wa maigirma gwamnanmu da muka zaba karkashin wannan jamiyya, sukunin gudanar da mulkinsa cikin tsanaki. Ba komai ne ya sa na ce haka ba, sai don ganin yadda har yanzu kawunan ‘ya‘yan jam’iyyar a jihar ya kasa haduwa waje daya. Hakan ya samo asali ne tun lokacin zaben  fitar da gwani na takarar gwamnan jihar. Kuma ya yi sanadiyyar raba wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar a wasu kananan hukumomin jihar da kujerunsu ba bisa ka‘ida ba, sakamakon suna goyon bayan wani bangare na jam’iyyar a jihar. Wani babban abin takaicin ma shi ne: Wannan rikici ba kowane ke kara ruruta shi ba, face shugabanni! da masu fada aji a cikin jam’iyyar APC a  jihar, wadda a ganinsu sai sun yi hakan ne, “miyar gidajensu za ta gyaru“. A gaskiya mu magoya bayan jam’iyyar a jihar, wannan abu yana kona mana rai matuka. Da wannan nake kira ga shugabancin jam’iyyar APC a matakin kasa, da su yi wa Allah su shigo Jihar Jigawa, don dinke dukkan rashin fahimtar junan, da ke cikin wannan jam’iyya a jihar. Domin abin da ke faruwa cikin jam’iyyar adawa ta PDP a matakin kasa da jihohi, ya ishemu ishara. A karshe ina  addu’ar Allah ya kara hada kawunanmu, amin-summa.
  Daga: Isah Ramin Hudu Hadejia. 08060353382 [email protected]

Addu’a ga Aminiya

Edita ni mai karanta jaridar Aminiya, Ubangaji Allah ya kare ku daga masharranta.  
Daga Sanusi Musa Police Gusau Jihar Zamfara

Ga Alhaji Aliko dangote
 Edita ba ni fili in mika godiyata ga shahararren dan kasuwar nan, mai taimako Alhaji Aliko dangote kan niyyarsa ta gina dakunan kwanan dalibai a ABU Zaria. Mun gode, Allah ya saka masa da alheri. Amin.
Daga Amiru Isa Bakori 07068147933  
Addu’a ga Gwamna Masari

Ina so in ja hankalin masu garaje a kan ganin Maigirma Gwamnan Jihar Katsina ya shimfida ayyuka a cikin gaggawa da su sani, cewa, gaggawa ba ita ce mafita ba. Abin da ya dace, shi ne, mu ci gaba da yi masa addu’a da fatan Allah ya iya musu, kuma ya ba su ikon sauke nauyin da ke kansu. Mu sani cewa fiyayyen halitta ya ce: ….”kuffa ‘alaika haaza”. Allah ya sa mu gane. Daga Abu Muhammad KTN
Kira ga Shugaba Buhari

Salam Aminiya don Allah ku ba ni dama in yi kira ga shugaban kasa a kan ’yan kabilar Igbo. Don Allah shugaban kasa, mu Hausawa mazauna Kudu maso Kudu muna fama da barazana daga ’yan kabilar Igbo masu rajin son kafa Biafra. Muna son ka sa idon a kan hakan, domin abin da suke yi mana yana nuna  on komawa fadan kabilanci.
Daga Aliyu Sanusi Jihar Zamfara 07067720769
Roko ga Gwamna el-Rufa’i

Assalam alaikum Aminiya. Don Allah ku rokar mini Malam Nasir El Rufa’i (Gwamnan Kaduna), game da hanyar danwata, da ke karamar Hukumar Soba, wadda ta tashi daga Rahama zuwa Danwata U/dan’iya, taka lafiya, Lungu zuwa Soba. Ko kuma Rahama,- danwata zuwa Kargi. Muna cikin wani hali na bukatar hanya. Ya mai girma Gwamna, in damina tayi mota ba ta iya shiga danwata sai dai Tarakata ta noma, ga shi muna fitar da amfanin gona cikin wahala.
Daga Abdulmalik Ja’afar danwata. 07030311081
A rika yi wa kasa addu’a

Aminiya, don Allah a mika min sakona ga malaman kasar nan. Don Allah ku dinga wayar wajmutane kai, ta yadda za a rika yi wa kasar mu addu’a. Allah ya raba mu da sharrin ‘Ja Ya dauko, ja ya kwache.
Kira ga Gwmnan  Zamfara

Don Allah a yi kira ga Gwamnan Jihar Zamfara ya taimaka, ya biya mana kudin jarabawar NECO da WAEC na shekarar 2013//14. Yau kusan shekara uku zaune a gida.
Daga Abba Zarumi Bello Gusau [email protected]
Gwamna Masari a tuna da talakawa

Salam Aminiya,ku ba ni dama in yi kira ga Maigirma (Gwamna Jihar Katsina) Rt. hon.Aminu Bello Masari. Don Allah ka tuna da talakawanka na Yammacin kankara wadanda ’yan bindiga suka matsa mawa.
Daga Mahammad Zayyana Mudi Tsamiyar Jinoo
A daina zagin Shugaba Buhari

Salam zuwa ga Aminiya. Don Allah mene ne sunan mutumin da ke zagin Shugaban kasa Buhari, rashin ilimi ne ko jahilchi ko adawa? Ya kamata mu yi hakuri mu ga me zai faru, amma sai zagi ya kamata mu daina. Da fatan Allah ya sa mu dace.
 Daga Sabon Sarkin Tudu Umar Bagwonde 08033205218.
Kira ga Gwamna Lolo

Assalam Edita wai don  Allah me na yi muku na rubuta kun ki bugawa. Don girman Allah ku taimaka ku buga mani wannan sako domin amfanin al ummarmu. Ina Gwamna Abu Lolo ina sanatanmu, ina wakilinmu ina membarmu wallahi ka da ku ci amanar al’ummar karamar Hukuma Katcha Allah zai kama ku, labari kawai muke ji wai ana ba da katin dan kasa mu ba ba mu ba ga asibiti ba, mu ba ga hanya ba; mu ba ga ruwa ba; mu ba ga wutar lantarki  ba Ku ji tsoron Allah.
Daga Haruna Ibrahim Katcha 08116467485.
Godiya ga Gwamna Tambuwal

Assalamu Alaikum Eidta jairda mu ta Aminiya barka da hakuri da mu. Don Allah ka ba ni dama in yi godiya ga maigirma gwamna Sakkwato. Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal, Matawale Garkuwan Lafiya, saboda hangen nesa da ya yi wajen bai wa Hon Musa Ausa Gidan Madi Tangaza Kwamishinan matasa da wasanni. Saboda ba a taba samun Kwamishina irin sa ba.
Daga M. Murtala Amwa. Tambuwal 2019. kanwuri sokk North  Nagode 08050332277.