✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya’yan APC a Kalaba sun yi shagulgulan murnar lashe zaben Shugaban Kasa

Magoya bayan Jam’iyyar APC da ke Nasarawa-Bakoko da kuma wadanda suke a Unguwar Hausawa, Layin Bagobiri a Kalaba, sun gudanar da shagulgulan samun nasarar Shugaba…

Magoya bayan Jam’iyyar APC da ke Nasarawa-Bakoko da kuma wadanda suke a Unguwar Hausawa, Layin Bagobiri a Kalaba, sun gudanar da shagulgulan samun nasarar Shugaba Buhari a zaben Shugaban Kasa da aka kammala ranar Asabar da ta gabata. Da yake yi wa Aminiya karin haske Kakakin Jamiyyar APC a Mazaba ta Daya a Karamar Hukumar Kalaba, Bala Yakubu ya bayyana dalilan da suka sanya su yin shagulgulan “Saboda murnar  Baba Buhari ya samu  nasarar lashe zabe karo na biyu shi ya sa muke wannan murna domin mu nuna goyon bayyanmu dari bisa dari da fatan Allah Ya taimake shi Ya taya shi riko,” inji shi.

Akasarin wadanda aka zanta da su a wuraren shagulgula na Nasarawa Bakoko da Unguwar Hausawan sun bayyana matukar farin cikinsu tare da fatan a ci gaba da ba Shugaban Kasa goyon baya da ta ya shi addu’ar Allah Ya ba shi ikon ci gaba da aikin da ya fara shekara a hudunsa na farko na tabbatar da tsaro da farfado da noma da tattalin arziki da kuma hada kan jama’a.