’Ya’yan marigayi Cif MKO Abiola, mutumin da ya lashe zaben shugaban kasa na 1993 guda biyu sun garzaya Babbar Kotun Jihar Legas da ke Ikeja suna neman a bi musu kadin zargin keta musu hakki da jami’an ’yan sanda suka yi.
Kassim Abiola da Aliyu Abiola dai suna nema hakkinsu ne bayan da aka cafke su bisa fashin da aka yi a gidan mahaifinsu ranar biyu ga watan Satumba tare da neman diyyar Naira miliyan saboda bata suna.
Sun dai nemi kotun da ta kwato musu hakkinsu bisa zargin cin zarafi da kuma keta musu haddi, suna masu cewa jami’an ’yan sandan SARS sun kama su ne bayan korafin da wata matar mahaifin nasu mai suna Adebisi Abiola ta yi a kansu bayan fashin.
A cikin kunshin karar da lauyansu kuma mai fafutukar kare hakkin dan-adam, Mike Ozekhome ya shigar dai, ’ya’yan Abiolan na karar kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas ne, kuma suna neman kotun da ta ayyana kamun da aka yi musu a matsayin haramtacce kuma ya take hakkinsu na walwala.
Baya ga neman a ba su hakuri, masu shigar da karar na kuma neman kotun da ta tilasta a biya su diyyar Naira miliyan 100 bisa keta hakkinsu da aka yi.
’Yan sanda a Jihar Legas ne dai suka kama mutanen biyu bisa fashin da aka yi a gidan mahaifin nasu.
Sun shaida wa kotun cewa da gangan aka ware su su biyu aka ci zarafin nasu don kawai matar mahaifin nasu ta zarge su da hadin baki a ciki.
Sun ce ’yan sanda sun bincika duk gidajensu amma ba a ga ko da abu kwaya daya mallakin matar ba a wajensu.
Kassim da Aliyu sun kuma musanta hannu a zargin da ake musu a fashin wanda suka bayyana a matsayin karya da kuma yunkurin bata sunansu da na iyalansu, tare da cewa ’yan sanda ba su da kowace dama ta tsare su sama da sa’o’i 24 ba tare da umarnin kotu ba.