Sojojin Najeriya sun ce ya zuwa yanzu, akalla kwamandoji da mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP 1,500 ne suka ajiye makamansu sannan suka mika wuya a yankin Arewa maso Gabas.
Ko a karshen makon nan sai da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda iyalan mayakan da dama, ciki har da mata da kananan yara suka bi layi sannan suka je gurin dakarun sojojin da ke Mafa a Jihar Borno domin mika wuya.
- Ayyukan ’yan bindiga ya ragu matuka a Katsina – Masari
- An tura tawagar bincike ta musamman kan kisan matafiya a Jos
Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa wasu manyan kwamandojin kungiyoyin ’yan ta’addan da suka hada da Adamu Rugurugu da iyalansa tuni suka mika kansu ga sojojin Najeriya a wurare daban-daban da aka kebe a Jihar ta Borno.
Wasu daga ciki mayakan dai sun mika wuyan ne tare da iyalansu a garuruwan Bama da Mafa da kuma Gwoza a karshen mako.
Kafar, ta kuma rawaito cewa yawan tallace-tallacen da rundunar sojojin Najeriya ta dauki nauyinsu a harsunan Hausa da Kanuri a ’yan kwanakin nan a yankin sun taka muhimmiyar rawa wajen ajiye makaman ’yan ta’addan.
Wata babbar majiya a sashen tattara bayanan sirri na rundunar sojojin ta ce mayakan na barin sansanoninsu suna mika wuya saboda irin wa’azin da malaman addinin Musulunci suke yi musu.
Majiyar ta kuma ce akalla mayaka 2,000 ne ake sa ran za su mika wuyan a yankin Tafkin Chadi nan ba da jimawa ba.
“Yawancinsu sun mika wuya kuma sun fice daga kungiyar saboda tallace-tallace da kuma wa’azin da malamai ke yi musu kan su bar mummunar akidar da suke kai.
“A zahirin gaskiya, mafi yawansu dama ko dai tilasta musu aka yi tun da farko, ko kuma jirkita tunaninsu aka yi lokacin da ayyukan ta’addanci ke kan ganiyarsu. Sun kuma mika makamai da dama kuma suna ba dakarunmu hadin kai yadda ya kamata,” inji majiya kamar yadda ta shaida wa PRNigeria.