✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji 5 da Lakurawa 6 sun mutu a musayar wuta a Sakkwato

An kashe mayakan Lakurawa shida da sojoji biyar a yayin wata musayar wuta a yankin Gudu da je Jihar Sakkwato

Sojoji sun bindige ’yan ta’addan Lakurawa akalla shida har lahira tare da kwato makaman bata-garin a  Jihar Sakkwato.

Daraktan Yada Labarai na Rundunar Operation Fansan Yamma, Laftanar-Kanar Abubakar Abdullahi, ya sanar a ranar Alhas cewa sojoji sun halaka ‘yan ta’addan ne a ranar Asabar da ta gabata ne sojoji suka yi artabu da su a Karamar Hukumar Gudu.

Ya ce sojoji sun yi araba da su ne a ci gaba da aikin da sojojin ke yi na kawar da Lakurawa a Jihar Sakkwato.

“Bayan musayar wutan an kashe ’yan ta’adda shida an kwato bindigogi kirar AK47 guda hudu da harsasai 160 nau’ika daban-daban daga hannunsu.

“Sai dai kuma mun rasa mutum biyar daga cikin dakarunmu a yayin musayar wutar,” in ji Laftanar-Kanar Abdullahi.

Ya bukaci al’umma da su rika lura tare da kai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro rahoton duk motsin da ba su yarda da shi ba.