✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yawan tsararrun da ke Jiran shari’a ne silar hare-hare a gidajen yari —Kungiya

PRAWA ta tattauna da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, a kan kiran da ya yi na gaggawar rage cinkoso a gidajen yari a Najeriya.

Kungiyar kula da walwala da gyaran halin tsararru (PRAWA) ta yi  kira ga gwamnati da ta dau mataki cikin gaggawa kan yawaitar tsararrun da ke jiran shari’a a gidajen yarin Najeriya.

Kiran na kunshe cikin wata sanarwa da daraktar Kungiyar PRAWA, Dokta Uju Agomoh ta fitar ranar Laraba a Abuja.

Agomoh ta ce a lokuta da dama tsarraun na daukar lokacin da idan shari’ar aka yi ba lallai hukuncin da za a yanke musu ya kai haka ba.

Ta ce PRAWA ta tattauna da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, a kan kiran da ya yi na gaggawar rage cinkoso a gidajen yari a Najeriya.

Agomoh ta ce kungiyar ta bibiyi shirin sake fasalin gidajen yari da gwamnati ke yi na kusan shekaru talatin zuwa yanzu, inda ta gano babban kalubalen gyaran shi ne tafiyar hawainiyar shari’ar tsararru.

Agomoh ya ce kwararru na alakanta yawan tsararrun da ke jiran shari’a, da cinkoso a gidajen yari a matsayin abin da ke tabarbara lamuran tsaro a kasar.

%d bloggers like this: