Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin wasu dillalai kan zargin shigo da jabun magunguna daga kasar waje da nufin sayarwa a Kano.
Hukumar Kula da Ingacin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) reshen Jihar Legas ce ta gurfanar da dillalan kan zargin aikata laifin a Jihar Legas, inda kotun ke zama.
- An Kori Dalibai 40 A Auchi Poly Kan Takardun Bogi
- D’banj: ‘Mu muka gayyaci ICPC kan badakalar N-Power’
Lauyan Hukumar NAFDAC, Barth Simon, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake zargin — wani Shugaban Kungiyar Kamfanonin Dillancin Magunguna a Kano da abokan sana’arsa biyu — sun shigo da wasu jabun magunguna daga ketare domin kaiwa Kano su sayar, wanda hakan ya saba wa dokokin kasa.
Sai dai duk wadanda ake tuhumar sun musanta zargin, daga nan lauyansu Ikechukwu Anima, ya roki kotun ta ba da belin su.
Kotun ta amince da rokon nasa sannan ta ba da belin kowannensu a kan Naira miliyan bakwai, tare da masu tsaya musu da suka mallaki kwatankwacin kudaden.
Daga nan alkalin kotun, Ayokule Faji, ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Maris, 2023.