An gurfanar da wasu mutane biyu a wata kotun majistare da ke garin Ado-Ekiti bisa zarginsu da satar littafin Baibul guda 20, da na wakokin Ibadar Kiristoci bakwai, da kuma littafin gadimin coci daya.
Wadanda ake zargin Basiru Abubakar mai shekaru 20, da Peter Friday mai shekaru 18, ana tuhumarsu ne da laifin hadin baki da kuma sata.
- Tikitin jirgin sama daga Abuja zuwa Kano ya sake kaiwa N135,000
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Burodi Ba Zai Daina Tsada Ba Yanzu
Dan Sanda mai gabatar da kara, Insfekta Oriyomi Akinwale ya bayyana wa kotun cewa mutanen sun aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Yuli da karfe 11:00 na safe a Cocin da ke unguwar Bank Rod a Ado-Ekitin.
Ya ce sun sace abubuwa da dama da suka hada da takardun likawa a bango, da takardun adana sadaka da suka kai na Naira Miliyan 150.
Kayan dai a cewar dan sandan mallakin wata Adedokun Esther ne, da ta yi holensu a wajen cocin domin sayarwa.
Ya ce laifin ya saba wa sashe na 302(1)(a) na kundin manyan laifukan jihar ta Ekiti na shekarar 2021.
Sai dai mutanen da ake zargin sun musanta aikata laifin.
Lauyarsu, Misis Funmilayo Akinwumi ta roki kotun da ta ba da belinsu kan sharudda marasa tsauri.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Bonkole Oluwasanmi ya ba da belinsu kan Naira 50,000 da kuma masu tsaya musu biyu da suka mallaki wannan kudin.
Daga nan ne ya dage shari’ar zuwa ranar biyu ga watan Satumban 2022.