Kungiyar kula da walwala da gyaran halin tsararru (PRAWA) ta yi kira ga gwamnati da ta dau mataki cikin gaggawa kan yawaitar tsararrun da ke jiran shari’a a gidajen yarin Najeriya.
Kiran na kunshe cikin wata sanarwa da daraktar Kungiyar PRAWA, Dokta Uju Agomoh ta fitar ranar Laraba a Abuja.
- Satar N1.4bn a banki: EFCC ta kama dan takarar Majalisar NNPP a Kogi
- Zan soke biyan kudin NECO da JAMB, zan dauki sojoji 750,000 —Kwankwaso
Agomoh ta ce a lokuta da dama tsarraun na daukar lokacin da idan shari’ar aka yi ba lallai hukuncin da za a yanke musu ya kai haka ba.
Ta ce PRAWA ta tattauna da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, a kan kiran da ya yi na gaggawar rage cinkoso a gidajen yari a Najeriya.
Agomoh ta ce kungiyar ta bibiyi shirin sake fasalin gidajen yari da gwamnati ke yi na kusan shekaru talatin zuwa yanzu, inda ta gano babban kalubalen gyaran shi ne tafiyar hawainiyar shari’ar tsararru.
Agomoh ya ce kwararru na alakanta yawan tsararrun da ke jiran shari’a, da cinkoso a gidajen yari a matsayin abin da ke tabarbara lamuran tsaro a kasar.