Yawan mutanen da suka mutu a sakamakon girgizar kasar nan da ta fada wa tsibirin Java na Indonesiya a makon da ya gabata yanzu sun kai mutum 321, kamar yadda Hukumar Kiyaye Bala’o’i ta Kasar ta tabbatar.
Girgizar kasar mai karfin dugo 5.6 ta fada wa yankin Cianjur da ke tsibirin ne ranar Litinin din da ta gabata, inda mutane da dama suka rasu, gine-gine masu yawa kuma suka rushe.
- ‘Ba da yawunmu ’yan fansho suka kai wa dan takarar Gwamnan Gombe na PDP ziyara ba’
- Tserarrun fursunoni sun yi garkuwa da lauya mace a Fatakwal
Shugaban Hukumar Kiyaye Bala’o’in, Suharyanto, ya shaida wa wani taron manema labarai ranar Lahadi cewa ma’aikatan ceto sun kuma gano karin gawarwaki uku, sai kuma wasu takwas ranar Asabar.
“Bayan gano karin gawarwaki uku a yau [Lahadi], yanzu yawan wadanda suka mutu sun kai 321 ke nan. Sai kuma wasu mutum 11 da har yanzu ba a san inda suke ba,” inji Suharyanto.
Masu aikin ceto za su dawo ranar Litinin, inda za su fi mayar da hankali a yankunan da ake zaton mutanen da suka mutu gine-gine sun danne su, kamar yadda jami’in hukumar ceto ta Yammacin Java, Jumarin, ya tabbatar.
Girgizar kasar dai ta lalata gidaje 62,000, sannan ta tilasta wa sama da mutum 73,000 barin gidajensu, inji Suharyanto.
Kakakin hukumar kiyaye bala’o’in, Abdul Muhari, ya ce hukumomi na shirin zama don tattaunawa a mako mai zuwa don duba yiwuwar tsawaita lokacin kai dauki sama da kwana 14 na farkon da aka saka tun da farko.
Kasar Indonesiya dai na yawan fuskantar bala’o’in girgizar kasa da kuma duwatsu masu aman wuta saboda yanayin da kasar ke ciki.