Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC ta yi hasashen cewa adadin yawan masu rajistar zabe zai iya karuwa daga miliyan 10 zuwa miliyan 80 a shekarar 2019.
Shugaban Hukumar Zabe mai zaman Kanta ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shi ne ya yi hasashen yayin wata tattaunawa da kwamitin bin diddigin zabe a Najeriya da Afirka ta Yamma na Kungiyar Tarayyar Turai ya shirya, a Abuja.
A wata takardar sanarwa da Babban Mai Magana Da Yawun Hukumar Zabe ta INEC, Mista Rotimi Oyekanmi ya sanya wa hannu a Abuja, ta nuna cewa kungiyoyi masu zaman kansu da dama da masu ruwa da tsaki a harkar zabe sun halarci taron.