Wasu iyalan makiyaya mafiyawa mata da kanan yara, da adadinsu ya kai 350 sun yi hijira daga yankinsu na Kuchi da ke Karamar hukumar Munya ta jihar Neja, zuwa garin Sabo Wuse da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, a cikin jihar.
Wakilinmu da ya ziyarci wajen a ranar Lahadi, ya ga yadda al’ummar ke zaune a wani fili da ke kusa da karamin ofishin ‘yan sanda da ke mashigar garin.
Wasu da suka zanta da Aminiya sun ce, sun baro yankin nasu ne bayan fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da suka ce sun kashe masu mutane da dama tare da sace wasu, na tsawon lokaci.
Daya daga cikin ‘yan tawagar mai suna Muhammad Lawan ya ce, wata daga cikin matan da suke tare ta haihu a cikin daya daga cikin motocin tirela 4 da suka dauko su, a lokacin da suke kan hanyar zuwa.
Haka nan ya ce, akwai wata matar kuma da ta haihu a wajen da suka kaman, bayan isowarsu.
Wani dattijo da ke matsayin jagoran jama’ar ya ce, sun baro kamar shanu dubu 1 a hannun matasa daga cikin mazajensu da suka nufi wani yankin na daban.
Ya ce, da farko sun yada zango ne a wani fili da ke yankin Karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna, amma sai wasu su ka tilasta masu barin wajen.
Ya ce, haka nan ‘yan sanda da ke sa ido a inda suke na yanzu sun bukaci da su bar wajen
Wani karin matsala da ya ce, sun fuskanta ita ce ta bukatar Naira dubu dari 500 da wasu da ya ce sun yi ikirarin cewa su jagorori ne na kungiyar Miyetti Allah na yankin daga wajensu, don sama masu wani waje da za su iya yin wata 1, kamar yadda ya yi bayani.
“To a dalilin wadannan sabbin matsaloli a yanzu muna shawarar wucewa garin Lafiya a jihar Nassarawa, inda muke da wasu ‘yan uwa, in ji jagoran tawagar.