✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaushe Jacob Zuma zai fara zaman kaso?

Jacob Zuma ya ce ba zai bi umarnin kotu na ya kai kanshi gidan yari ba

Tsohon Shugaban Kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, wanda aka baiwa umarni ya mika kanshi don fara zaman kaso na wata 15 saboda raina kotu, ya ce ba za ta sabu ba.

Mista Zuma ya fadi hakan ne ranar Lahadi a gidansa dake lardin Kwa-Zulu Natal, wato Nkandla, inda dimbin magoya bayansa suka taru don ba shi kwarin gwiwa.

Ya shaida wa ‘yan jarida cewa, “Babu abin da zai kai ni gidan yari a yau”.

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa, “Ba zai yiwu su karbi takardu ba sannan su sa ran zan tafi gidan kaso”, yana mai nuni da daukaka karar da ya yi yana kalubalantar hukuncin.

‘Tamkar hukuncin kisa’

“Aikewa da ni gidan yari a shekaruna kuma a lokacin annoba tamkar hukuncin kisa ne”, inji shi.

Tun da farko dai, tsohon shugaban mai shekara 79 a duniya ya shaida wa magoya bayansa cewa alkalan kotun tsarin mulki ta kasar sun “keta min hakkokin da kundin tsarin mulki ya ba ni”.

Mista Zuma ya kuma ce shi da lauyoyinsa sun rubuta wa kotun takarda suna cewa hukuncin bai dace ba, a yunkurin da suke yi na ganin an rage ko ma an soke shi baki daya.

Ya kuma jagoranci magoya bayansa wajen rera wakar nan ta adawa da mulkin wariyar launin fata, wato “Umshini Wami” (Kawo Min Bindigata Mai Sarrafa Kanta).

Magoya bayan Mista Zuma sun sha alwashin hana mahukunta kwanciyar hankali idan aka kai shi gidan kaso..

Taurin kai

Ranar Talata aka yanke wa Mista Zuma hukuncin saboda samun shi da laifin raina kotu bayan da ya ki bayyana a lokuta da dama a gaban masu binciken almundahana don bayar da shaida.

Tuni dai kwamitin binciken, wanda aka kafa a 2018 don ya gano gaskiyar zarge-zargen da ake yi cewa tsohon shugaban kasar ya yi sama da fadi da dukiyar kasa, ya saurari bahasi daga wurin shaidu 40.

Kwana biyar kotun ta ba Zuma ya mika kansa ga hukumomi. Ranar Lahadi kuma wa’adin ya cika.

Duk da hukuncin dai, kotun ta amince ta saurari karar da ya daukaka yana neman a soke umarnin, ta kuma ce ranar 12 ga watan Yuli za ta zauna don haka.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wata malamar jami’a mai koyar da shari’a, Cathleen Powell, tana cewa daukaka karar da Mista Zuma ya yi ba za ta jingine hukuncin kotun ba.

Tauna tsakuwa…

A wani mataki na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, magoya bayan Zuma sun yi makonni suna zaman dirshan a kofar gidansa sanye da kaya masu tambarin jam’iyyar ANC.

“Da na ga ‘yan sanda a nan sai da na tambayi kaina, ‘yaya za a yi su iso inda nake; yaya za su yi su keto ta cikin wadannan mutanen?'”, inji Zuma, yana yin ba’a ga hukumomin Afirka ta Kudu.

Daya daga cikin magoya bayan tsohon shugaban, Lindokuhle Maphalala, ya fada wa AFP cewa, “Idan [Ministan Al’amuran ‘Yan Sanda] Bheki Cele ya zo nan don kama uBaba (Zuma) to sai dai ya fara da mu.”

Magoya bayan na Mista Zuma sun lashi takobin kare shi, suna kira ga Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi murabus.

ANC ta sa baki

A karshen mako jam’iyyar ANC ta tura wakilai su gana da Mista Zuma a gidansa (wanda aka yiwa kwaskwarima da kudin baitul malin gwamnati Dalar Amurka miliyan 24 lokacin yana kan kujerar mulki).

Jam’iyyar ta soke wani taron Kwamitin Zartarwarta saboda abin da ta kira kiki-kakar da ake fuskanta a Kwazulu Natal.

Baya ga fuskantar kwamitin da ke bincike a kansa, an kuma zargi Zuma da hannu dumu-dumu a wata badakalar cin-hanci shekaru fiye da 20 da suka gabata.

Mista Zuma na fuskantar tuhume-tuhume 16 da suka shafi zamba cikin aminci, da almundahana, da cuwa-cuwa, wadanda suka danaganci sayen wasu jiragen saman yaki, da jiragen ruwa na sintiri, da sauran kayan yaki daga wasu kamfanonin Turai biyar a kan kudi Rand biliyan 30, wadanda a lokacin suka kai kwatankwacin Dala biliyan biyar.