A yau Juma’a 18 ga Maris, 2016 ne ake sa ran za a gudanar da jadawalin gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) matakin kusa da na karshe Kwata-Fainal.
kungiyoyin kwallon kafa takwas ne suka kai wannan matsayi da suka hada da Real Madrid na Sifen da PSG na Faransa da Wolssburg na Jamus da Benfica na Fotugal da Manchester City na Ingila da Atletico Madrid na Sifen da FC Barcelona na Sifen da kuma FC Bayern Munic na Jamus.
Jadawalin ya nuna kowane kulob zai iya haduwa da wani, ko da kuwa sun fito daga kasa daya ne.
Alal misali Real Madrid za ta iya haduwa da Atletico Madrid ko FC Barcelona da suka fito daga kasar Sifen ko Bayren Munich za ta iya haduwa da takwararta Wolfsburg da suka fito daga Jamus.
Za a gudanar da jadawalin ne a bainar jama’a a hedkwatar hukumar da ke Zurich na kasar Suwizilan. Sannan bikin zai gudana ne da misalin karfe 12 na rana agogon Najeriya.
Bayan an gudanar da jadawalin ana sa ran za a fara wasan farko ne a ranakun 5 da 6 ga watan gobe (Afrilu) yayin da wasa na biyu kuma zai gudana ne a ranakun 12 da 13 na watan gobe (Afrilu).
kungiyoyin hudu da suka samu nasara za su kai matakin kusa da na karshe watau Semi-Fainal. Sannan za a yi wasan karshe ne a ranar 28 ga watan Mayun, 2016 a filin wasa na kulob din AC Milan da ke Italiya.
FC Barcelona na Sifen ce take rike da kofin, kuma babu wata kungiya da ta taka lashe gasar sau biyu a jere tun bayan da aka sake wa gasar suna zuwa gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai (UEFA Champions League) a shekarar 2000.
Kulob din Real Madrid ne ya fi yawan lashe gasar har sau 10.
Yau za a yi jadawalin kwata-fainal na gasar zakarun kulob na Turai
A yau Juma’a 18 ga Maris, 2016 ne ake sa ran za a gudanar da jadawalin gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League)…