✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya kaurace wa zaman shari’ar zargin sa da rashawa

Lauyoyi sun hallara a kotu inda gwamnatin Kano za ta gurfanar da tsohon gwaman jihar, Abdullahi Ganduje, kan zargin badakalar kudade

Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da iyalansa sun kaurace wa zaman shari’ar da gwamnatin ke zargin su da badakalar kudade.

Gwamnatin jihar mai ci ta maka na zargin Ganduje da iyalansa da wasu makusantansa da cin hanci da rashawa da karkatar da dukiyar al’umma.

ِAna shari’ar ne a Babbar Kotu Mai Lamba Hudu da ke Sakatariyar Audu Bako a Kano, inda aka sa ran gurfanar da Ganduje, wanda kawo yanzu babu tabbacin ko zai halarci zaman da za a fara saurara.

Hukumar yaki da almundahana ta jihar Kano, na zargin Ganduje ne da laifuka guda takwas.

Shugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce hukumar ta gano wata badakalar karkatar da kudaden kanana hukumomi Naira biliyan 51.3 a zaman mulkin Ganduje.

Haka kuma hukumar na zargin zargin fitar da kimanin Naira miliyan 600 daga asusun gwamnatin Kano zuwa wani kamfani da tsohon gwamnan yake darakta kuma mai dakinsa ke gudanar da asusunsa.

Muhuyi ya ce sun shirya gabatar da shaidu 15 da kuma hujjojin da ke nuna alakar tsohon gwamnan da laifuffuka da ake zargin sa.

Wasu dai na zargin zargin da hukumar ke wa Ganduje da iyalinsa ramuwar gayya ce kan dakatarwar da ya yi wa shugaban hukumar, amma Muhyi ya musanta zargin da cewa tun Ganduje na mulki hukumar ta fara aiki kan lamarin, wanda shi ne ma dalilin da ya sa aka dakatar da shi.

“Bincike muki kan wasu abubuwa da iyalinsa suke, kuma su ba su karyata ba, babu wanda ya fito daga gwamnati ya ƙaryata

“Kuma abin da aka ce an dakatar da ni a kan shi, ba a iya tabbatar da shi ba har kotu ta ce mu dawo.” a cewar Muhuyi.

A zamnin mulkin Ganduje dai ya sha musana zargin da ake masa, har ya sanar cewa an kafa kwamiin binciken wani bidiyon da ke zargin yana karbar Dala yana cusawa a aljihu, domin hukuna duk wanda aka samu da laifi.

Gurfanar da shin da ake shirin yi na zuwa ne kwana biyu rak bayan dakaawar da wasu da ba a sani ba suka ce sun yi wa Ganduje daga jam’iyyarsa a APC, a mazabarsa, da ke Karamar Hukumar Dawakin ofa a Jihar.

Shugabancin APC na jihar dai ya yi wasi da dakarwar a masayin makircin yan adawa are da barazanar daukar maakin shari’a kan wadanda ke ikirarin dakaar da Ganduje, wanda shi ne shugaban jam’iyyar na kasa.