✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a fara gasar Olamfik

A yau Juma’a ne ake sa ran za a fara gasar wasanni ta Olamfik.  Gasar Olamfik, gasa ce wacce babu kamarta a tsakanin gasannin da…

A yau Juma’a ne ake sa ran za a fara gasar wasanni ta Olamfik.  Gasar Olamfik, gasa ce wacce babu kamarta a tsakanin gasannin da ake yi a duk fadin duniya.
Gasar, wacce za ta gudana a kasar Brazil kimanin kasashe 206 ne za su fafata a a cikinta.  sannan kimanin ’yan wasa dubu 11 da 178 ne za su halarci gasar da suka fito daga kasashe daban-daban na duniya.  Haka kuma za a fafata ne a wasanni dadaban-daban har 306.
Brazil mai masaukin baki ita ce take da mafi wakilci inda ’yan wasanta kimanin 464 ne za su fafata.  Sai Jamus mai ’yan wasa 420 sai Chaina mai ’yan wasa 398 sai Ingila mai dauke da ’yan wasa 366.
Najeriya tana da wakilcin ’yan wasa 75 ne yayin da Nijar take da wakilcin ’yan wasa 5 ita kuma Sudan ta Kudu tana da wakilcin wakilai 3 ne kaal a gasar. A Nahiyar Afirka, Somaliya ce take da mafi karancin wakilai inda take da ’yan wasa biyu kacal. Sannan a tarihin gasar, wannan shi ne karo na farko da kasashen Sudan ta Kudu da Kosobo za su fafata a gasar.
Gasar za ta fara ne daga yau 5 ga Agusta zuwa 21 ga watan idan Allah Ya kaimu.
Daga cikin wasannin da za a fafata a gasar sun hada da guje-guje da tsalle-tsalle da ninkaya da kwallon kwando da kwallon kafa (bangaren maza da mata) da kwallon gora da gudun fanfalaki (marathon) da gudun kwale-kwale, da gudun dawakai da daga karfe mai nauyi, da damben boksin da sauransu.
Kimanin shekaru 20 da suka wuce ne Najeriya ta zama zakara a fagen kwallon kafa, bayan ta lashe lambar zinari a tarihin gasar da aka yi a Atlanta ta Amurka.  Brazil ba ta taba lashe lambar zinare a bangaren kwallon kafa na maza ba, don haka ne a wannan karon za ta yi kokarin ganin ta lashe, musamman ganin cewa ana gudanar da gasar ce a kasarta.
Usain Bolt shi ne zakara a bangaren masu yin tsere kuma kawo yanzu
Usain Bolt shi ne zakara a bangaren guje-guje inda kawo yanzu babu wanda ya kama kafarsa.