A yau ne kotun Musulunci da ke Kano za ta ci gaba da shari’ar jarumar TikTok Ramlat Mohammed da aka kai gidan yari kan zargin karuwanci da badala.
A daren Juma’a ne kotun Musulunci da ke unguwar Sharada ta ba da umarnin tisa keyar Ramlat zuwa gidan yari bayan Hukumar Hisbah ta gurfanar da ita.
Mai Shari’a Sani Tanimu Hausawa ya ba da umanrin ne bayan Hisbah ta zarge ta da Tiktok wajen tana yin kalaman badala.
bidiyon Ramlat ta karade soshiyal midiya ne bayan ta yi wani bidiyo a Tiktok , wanda a ciki take tallata madigo, har take bayyana kanta a matsayin ’yar madigo.
- Murja Kunya ta yi layar zana daga gidan yari a Kano
- ’Yan ta’adda sun fara yaudarar kananan yara zuwa cikinsu
A cikin bidiyon, an ji matashiyar na cewa, duk wanda ai aure ta, to dole sai ya amince cewa ita za ta auro tata matar, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
A cikin wani bidiyonta bayan da Hisbah ta kama ta, matashiyar ta tabbatar cewa ita ce a cikin bidiyon, kuma gaske ita ce ta fadi wadannan maganganu.
Takardar karar da aka gurfanar da ita ta zargi Ramlta da amfani da Tiktok wajen yada badala, wanda hakan laifi ne a sashe na 341 da 275 da 227 na Kundin Pinal Kod.
Sai dai wacce ake zargin ta amsa laifukan inda ta nemi afuwar kotu bisa laifukan da ta aikata.
Sai dai saboda kurewar lokaci kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 19 ga Fabrairu don yanke hukunci.
Haka kuma kotun ta yi umarnin tisa keyar Ramlat zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar da za a sake dawowa gaban kotun.