✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau wa’addin girbi da Lakurawa suka ba manoman Sakkwato ke karewa

A Juma’ar nan wa’adin girbe amfanin gona da mayakan Lakurwa da ke shirin sakin dabbobinsu, suka ba wa al’ummar Jihar Sakkwato ke cika

A Juma’ar nan wa’adin girbe amfanin gona da mayakan Lakurwa da ke shirin sakin dabbobinsu, suka ba wa al’ummar Jihar Sakkwato ke cika.

Masu ikirarin jihadin da suka bulla a yankin yammacin Sakkwato dai na kara zama barazana ga al’ummar jihar da makwabtanta da tun kafin yanzu suke fama da ’yan fashin daji.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “duk wanda ka gani dauke da bindiga biyu za ka gan su, masu garkuwa da mutane suna tsoron su don sun fi karfinsu, ana kiran su daLakurawa masu jihadi.”

Ya ci gaba da cewa, “sun takura mutane sun hana wasu kauyuka noma, waddanda suka aminta su yi noman yanzu sun ba da kwana 70 kowa ya cire amfanin gonarsa domin za su saki dabbobinsu.

“A yanzu maganar da nake da kai sun rage kwanakin zuwa kwana 10, a wannan Jumu’a ta satin nan wa’adin zai cika, je ka ga yadda mutanen garin Alkasuna da Wariya da Kandam ke cire amfanin gonarsu babu shiri.

“Za ka ga wake fari fes an cire shi domin karamar hasara ta fi babba, wasu sun bar dawarsu a gona don ba ta kai girbi ba, ya rage nasu su bar ta, ko su sanya dabbobi su cinye,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.

Suna da jirage marasa matuki

“Dajin Bauri da Sarma da Kaidafi da Kandan su ne inda babbar dabarsu take yankin, kuma suna da yawa, an ce sun fi su 200,” a cewar wani mazaunin jihar.

Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Abdu Bulama Bukarti, ya yi zargin Lakurawa “na kafa manyan sansanoni kuma suna da muggan makamai, har da jirage marasa matuki suke amfani da su wajen yin sintiri a kan kauyuka da sansanonin soji.”

A cewarsa, mayakan kasar wajen sun kwace aikin sarakunan gargajiya kuma sun kai shekaru shida a Nijeriya sannan suna da hadari saboda akidarsu daya da ta Boko Haram da ISWAP, don haka, “Ya kamata a gaggauta daukar mataki, domin ina tsoron nan ba da jimawa ba, za su sama babbar barazanar tsaro.”

“Babu karamar hukumar Jihar Kebbi da babu su, kuma sun karde iko a kauyukan da ke wajen hedikwatar kananan hukumomin. Da wuya ka yi tafiyar kilomita biyar ba tare da hadu da su ba.

“Yanzu su ke wa mazauna wurare alkalanci, idan an samu sabani ko rikici, wurinsu ake kai kara saboda sun haramta wa sarakunan gargajiya sanya baki kan duk rikicin da aka kawo musu.

“Sarakunan ba su da zabi face su bi, saboda idan suka bijire wa umarnin za su rasa ransu.”

Ya ce, “Haka Boko Haram ta bunkasa ta zama kungiyar ta’addanci ta kasa da kasa ne saboda ba a dauki mataki da wuri ba, sai da ta yi shekaru tana harkokinta. Ga shi ta samu kwarewa ta tara makamai da kudaden ta hanyar ayyukan ta’addanci.

Yadda suka shigo Nijeriya

Mazauna Jihar Sakkwato sun bayyana cewa gayyato masu tsattsauran ra’ayin addini daga kasasashen waje, wadanda aka fi sani da Lakurwa aka yi zuwa Nijeriya.

Sun shaida wa Aminiya cewa asali gayyato Lakurawa aka yi zuwa Nijeriya, kuma tun a shekarar 2018 suka fara yin kaka gida a Dajin Gongono a Karamar Hukumar Tangaza.

Sun ce mutanen sun zo ne a bisa gayyatar su da Fulani makiyaya da ke yankin suka yi, domin su kare su daga barayin shanu da mutane, kasancewar a lokacin, ’yan fashin dajin sun addabi yankin Sakkwato da Zamfara.

Sun ce mayakan sun zo ne daga kasashen Aljeriya da Mali inda suke gudanar da abubuwa masu kama da aikin addini da kokarin hana barna, kuma tun wancan lokacin, suna hana shan sigari da dukkan kayan maye sun hana aske gemu da hana take wando, sun wajabta wa mata sanya hijabi, sannan suna karbar zakka a hannun Fulanin da ke da shanu masu yawa.

Dawowa suka yi

Bayan samun bayanansu da kuma barazanar da suke yi da kokarin karbar iko a yankin a wancan lokacin, jami’an tsaro da goyon bayan Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal suka samu nasarar korar su daga dajin.

Daga bisani Lakurawan suka sake dawowa dajin, wanda wuri ne da yake kan iyakar Nijar da Nijeriya, inda su kuma kasashen Aljeriya da Mali suke da iyaka a tsakaninsu.

Aminiya ta gano cewa mayakan suna kokarin samar da wani sansani nasu domin gina tsattsauran ra’ayin addini, shi ya sa suka fadada wurare da suke shiga har zuwa Jihar Kebbi.

Suna jan ra’ayin matasa

Shugaban Karamar Hukumar Tangaza, Alhaji Isa Salihu Kalanjeni, ya koka bisa yadda mutanen suke yaudarar matasa, suna ba su Naira miliyan daya domin su shiga kungiyar tasu.

Ya ce mutanen suna yin wa’azi ne tare da sanya dokoki a kauyukkan da ke makwabta da su.

“Mutanen sukan shigo cikin gari da rana su yi huldarsu, da dare su koma cikin daji.”

“Mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato, Idris Muhammad Gobir, ya yi magana kansu ya karkato da hankali don sanin abin da suke yi a in da suka yi kaka-gida,” in ji shi.

Kananan hukumomin Gudu da Tangaza nan ne ’yan bindigar suke zaune a tare da al’umma musamman a garin Goni da Sarma a Gudumar Ruwa Wuri a karamar hukumar Tangaza.

’Yan bindiga na tsoron su

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa, “mutanen ba su cika takura ba, kuma suna kare mutanen kauyukka daga barayin shanu da ke garkuwa da mutane, ba su jituwa da jami’an tsaron Nijeriya, harkokin addini suke yi duk in da suka zo, da baburan tsere suke amfani a cikin yankunanmu.”

“Dajin Bauri da Sarma da Kaidafi da Kandan su ne inda babbar dabarsu take yankin, suna da yawa, an ce sun fi su 200, kuma duk wanda ka gani dauke da bindiga biyu za ka gan su, masu garkuwa da mutane suna tsoron su don sun fi karfinsu, ana kiran su da Lakurawa masu jihadi,” in ji shi.
Sun addabi al’umma

“Mutanen suna da ra’ayin ba a sha da sayar da sigari, duk suka kama shagon da ake sayar da sigari za a karbe tare da yi masa gargadi, ba a sauraren komai a waya sai wa’azi, duk wanda suka kama yana sauraren wakoki ko kallon fim na Hausa za a yi masa hukunci da zai shafi duka ko rasa wayarsa,” a cewar mutumin da yake zaune a yankin.

Ya ci gaba da cewa, “mutanen akwai masu jin Hausa a cikinsu amma harshen da suka fi furtawa Fulatanci ne da Faransanci.

“Mutanen sun tara dabbobi da yawa a yankinmu, sun shigo yankin ba tare da komai ba, sun samu dabbobin ne ta hanyar karbar da Zakkah da suke yi.

“Duk Bafillacen da ke da dabbobi da yawa sukan fitar masa dakka su baiwa kansu, in ya ki aminta da fitarwa sai su karbe dabbobinsa gaba daya.

“Amma idan ’yan bindiga masu garkuwa suka kwace dabbobin mutum sukan karbo su a bai wa mai abu abinsa, ba su kaiwa gari hari, matsalar su da mutane su saba sharadinsu,” a cewarsa.

Sun mamaye kananan hukumomi biyar — Gwamnati

Mataimakin Gwamnan Sakkwato, Idris Gobir, ya bayyana cewa kungiyar mai na da makamai masu hadari, kuma sun mamaye kananan hukumomi biyar na jihar.

A cewarsa wannan abin takaici ne ke faruwa a Sakkwato bayan fama da take yi da ’yan bindiga masu satar mutane da dabbobi.

Alhaji Idris Gobir ya ce suna aiki tare da jami’an tsaro su tabbatar da kawar da matsalar don kare rayuwa da dukiyoyin al’ummar jiha.

Alhaji Sani Yakubu, Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gudu da Tangaza ya ce yankinsa ya dade yana fama da Lakuwara.

Zargin kashe basarake

Ya bayyaan cewa ana zargin su ne suka kashe ubankasar Balle a shekarun baya, domin tsawon lokaci suna zuwa karamar hukumar Gudu, amma ba su yi yawa kamar yanzu ba.

Ya ce, “wani lokaci sukan zo su yi sati ko wata ne su bar wurin. Tun lokacin da ake yakar su a kasar Mali sukan zo nan dajin Balle su labe daga baya su tafi.

“Tun bayan daminar nan suke cikin Gudu sun yi sansani a dukkan gefen Gudu kusan babu wani gari da ba karkashin ikonsu yake ba, sai Balle kadai.

“A kullum suna fadadawa, a yanzu sun shiga kananan hukumomi Binji da Tangaza da Silame, ba su cikin Jihar Kebbi don an koro su a can.

“Rayuwa na yi wa mutanen mu wahala, saboda mafi yawansu manoma ne, amma dajin ya zama mafakar mutanen da ke cewa masu jihadi ne da kuma ’yan bindiga; mutane na shan wuyarsu tun a 2018 har yanzu gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba.

Ya yi kira ga Gwamnatin Sakkwato karkashin Gwamna Ahmad Aliyu ta hadakarfi da jami’an tsaro a fitar da mutanen daga yankin kar su yi karfin da za a kasa yakar su.

A satin da ya gabata hedikwatar tsaron kasa ta fitar da bayani kan ’yan ta’addar da suka haifar da fargaba a jihohin Sakkwato da Kebbi.

Sun fara kai hari a Kebbi

Ana iya tuna cewa ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne sun kashe mutane 17 a a garin Mera da ke karamar hukumar Augie a Jihar Kebbi a Jumu’a da ta gabata inda suka saci shanu.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutanen sun shigo garin da misalin karfe daya na dare suka saci shanun mutane kuma da mutane suka yi kokarin kwato dabbobin maharan suka kashe mutane 17.

Ya ce, “a baya garin baya fama da matsalar tsaro sai da wadannan ’yan bindigar suka shigo har suka tafi da shanunmu bayan sun kashe al’umma.”

Bayan halartar sallar jana’izar mutanen, mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Sanata Umar Abubakar Tafida ya ce gwamnatin jiha za ta yi aiki sosai da jami’an tsaro don tabbatar da irin haka ba zai sake faruwa ba.

Sarkin Argungu ya nemi al’umma su hada kansu a rika bayar da bayani abin da ba a gamsu da shi ba a wajen jami’an tsaro don a tabbatar da an kare jama’a.

Za mu fatattake su — Sojoji

Kakakin rundunar tsaro, Manjo-Janar Edward Buba ya ce a wani hari da jiragen soji suka kai a yankin da ke iyakar jihar Zamfara da Kebbi, an kashe Lakurawa da dama da kuma ’yan fashin daji.

A cewarsa, sojoji sun san inda mutanen suke, kuma za su fuskance su u kora su waje.

Ya ce kungiyar nada alaka da ISIS, kuma a lokacin da suka shigo mutanen Kebbi da Sakkwato, shiru suka yi, sai da bata-garin suka fara gudanar da mummunan nufinsu ne suka yi magana a kansu.