Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce a ranar Alhamis zai mika kansa ga wani gidan yari da ke Jihar Georgia ta kasar, bisa zarge-zargen da ake masa na tayar da rikicin zabe.
Wannan ne dai karo na hudu da za a yanke wa Trump hukunci a jerin tuhume-tuhume a kararraki har guda hudu daban-daban, a daidai lokacin da yake yakin neman zaben sake darewar Shugabancin kasar.
- Dubban ’yan Afirka masu neman zuwa Turai sun makale a Nijar
- Mutum 2 sun rasu, 37 sun jikkata a benen da ya rushe a Abuja
Trump mai kimanin shekara 77 a duniya dai za a tsare shi ne a gidan yarin yankin Fulton da ke birnin Atlanta, kan zargin hada baki da wasu mutum 18 wajen yunkurin canza sakamakon zaben 2020 na kasar.
Tsohon shugaban dai ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, yana mai bayyana su da soki-burutsu.
Ya yi zargin cewa shugaba Joe Biden mai ci ya saka bangaren shari’a a alaihi, sannan yana kokarin amfani da shi wajen yi wa yunkurinsa na sake tsayawa takara kafar angulu.
Tuni dai aka tsarara matakan tsaro a gidan yarin na Fulton gabanin kamaTrump. Yanzu haka ma ana bincike kan mutuwar wasu daurarru a gidan yarin sakamakon cunkoso a ciki.
Babban mai shigar da kara na yankin na Fulton, Fani Willis, wanda shi ne ya maka Trump din a kotu, ya ce sun ba shi nan da karfe 5:00 na yammacin Juma’a ya mika kansa, ko su kama shi.
Ba a dai fadi takamaiman lokacin kama shi ba, amma ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta mai suna Truth cewa zai kai kansa da ranar Alhamis.