A wannan Asabar din, 18 ga watan Maris, 2023 ’yan Najeriya ke zaben gwamnoni a wasu jihohi 28 da ke fadin kasar.
A halin yanzu, ‘yan takarar kujerar gwamna 837 ne za su fafata a zaben da ke wakana a jihohi 28 daga cikin 36, sannan akwai ‘yan takara dubu 10 da 240 da za su fafata wajen neman lashe kujerun ‘yan majalisar dokoki 993 a mazabu dubu 1 da 21 da ake da su a fadin kasar.
Jihohi 28 da ke zaben gwamna
Jihohi 28 da zaben ke gudana sun hada da; Abiya, Adamawa, Akwa Ibom, Bauchi, Benuwe, Borno, Kuros Riba da Delta.
Sauran sun hada da Ebonyi, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Oyo, Filato, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe da Zamfara.
Dalilan da zaben gwamna ba zai gudana a jihohi takwas ba
A cewar Hukumar Zabe ta Kasa INEC, akwai kuma wasu jihohi 8 da ba za a gudanar da zaben gwamnoni a cikin su ba da suka hada da Anambra da Bayelsa da Edo da Ekiti da Imo da Kogi da Ondo da kuma Osun.
Wannan ya biyo bayan hukuncin kotu na rushe wasu zabuka da aka yi a baya tare da tabbatar da wasu da aka zaba wadanda da farko ba su aka bayyana ba a matsayin masu nasara.
Sai dai a duka jihohin za a gudanar da zaben ’yan majalisun jiha kamar yadda aka tsara tun da fari.
Wannan rashin daidaiton zabe tsakanin jihohin shida da sauran jihohin kasar ya zamar wa Hukumar Zabe ta INEC wani abu na koma baya, ganin kowacce jiha sai dai a yi mata nata shirin daban.
Hakan dai ya samo asali ne tun a 2003 lokacin da aka gudanar da zaben Jihar Anambra a watan Afrilu.
An bayyana Chris Ngige na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe, aka kuma rantsar da shi a matsayin gwamna ranar 29 ga watan Mayu na 2023, tare da duk wanda aka zaba.
A wannan lokaci Peter Obi ne ke takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APGA, ya nuna bai gamsu da wannan sakamako ba, abin da ya kai shi ga shigar da kara gaban kotu kenan.
Bayan shekara uku ya samu nasara kan shari’ar da ya shigar gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zabe, a karshe dai a watan Maris na 2006 a ka rantsar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben jihar.
Ko da aka zo gudanar da zabe a 2007, Obi bai shiga zaben ba, hakan ya sanya aka bayyana Andy Uba a matsayin wanda ya lashe zaben karkashin jam’iyyar PDP.
Daga baya kotu ta kara yanke hukuncin cewa Obi ne gwamna domin wa’adin mulkinsa bai kare ba, ta kuma yi bayani kan cewa “ wa’adin gwamna na farawa ne kawai daga ranar da aka rantsar da shi,” in ji kotu.
Tun daga wannan lokaci ne aka samu sabani wajen gudanar da zabe a jihar ta Anambra.
Irin wannan lamari ne ya faru a Jihar Edo a ranar 14 ga watan Afrilun 2007, lokacin da Kotun Sauraron Kararrakin Zaben ta ayyana Adams Oshiomhole a matsayin wanda ya lashe zaben jihar kuma ’yantaccen gwamna.
A 2010 ma, haka aka yi lokacin da kotu ta ayyana Kayode Fayemi a matsayin gwamnan Ekiti, ba a sake zabe a jihar ba sai 2014, maimakon 2011.
A watan Agustan 2008, kota a Jihar Ondo ta ayyana Dokta Olusegun Mimiko na jam’iyyar LP a matsayin gwamnan da ya lashe zaben jihar.
Kotun ta kwace mulki ne daga hannun Olusegun Agagu na jam’iyyar PDP wanda aka rantsar tare da sauran wadanda suka ci mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2007.
Irin wadannan tarin matsaloli da shari’u ne suka taru suka haifar da jinkiri a wajen daidaita zabe tsakanin wadannan jihoji da sauran da za a gudanar da zabensu a ranar Asabar 18 ga watan Maris.
Jihohin da gwamnoninsu ke neman tazarce
Akwai jihohi 11 da suka hada da Legas da Ogun da Oyo da Kwara da Zamfara da Gombe da Nasarawa da Yobe da Borno da Adamawa da kuma Bauchi da gwamnoni ke neman tazarce.
Jihohi da ke zaben sabbin gwamnoni
A halin yanzu akwai jihohi 17 da za su yi sabbin angwaye kasancewar gwamnoninsu duk sun kammala wa’adin zamani biyu da Kundin Tsarin Mulki ya tanada.
Jihohin sun hada da; Abiya, Akwa Ibom, Benuwe, Kuros Riba, Delta, Ebonyi, Enugu, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Neja, Filato, Ribas, Sakkwato da Taraba.
Gwamnoni da suka sha kasa a takarar Sanata
Daga cikin gwamnoni 17 da suka kammala wa’adinsu, 9 sun yi takarar kujerar Sanata a zaben da ya gudana ranar 25 ga watan Fabrairu, sai dai bakwai ne daga cikinsu ba su samu nasarar kai bantensu ba.
Gwamnonin sun hada da: Samuel Ortom na Benuwe, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Okezie Ikpeazu na Abiya, Darius Ishaku na Taraba, Simon Lalong na Filato, Ben Ayade na Kuros Riba da Atiku Bagudu na Kebbi.
Me zaben ke tafe da shi ?
Toh sai dai gabanin isowar ranar zaben, an samu rahotannin rikice-rikece musamman a jihohin da gwamnoninsu ke neman zarcewa.
Zaben gwamna a jihohin Kaduna da Filato da kuma Taraba na daukar hankali ta yadda wasu magoya bayan ‘yan takara ke amfani da kalaman nuna banbancin addini wajen sukar juna.
A jihohin Lagos da Zamfara da Oyo da Ogun da Bauchi da kuma Nasarawa, gwamnoninsu na fustantar babbar barazana daga bangaren ’yan adawa wadanda ke neman raba su da kujerunsu.
Jihar Kano, wacce ake kallo a matsayin cibiyar siyasar arewacin Najeriya, jam’iyar APC da ke mulkin ta ne ke fuskantar babbar barazana daga bangaren jam’iyyar NNPP ganin yadda ta lashe kujerun sanatoci biyu daga cikin uku da ake da su a jihar, tare da Majalisar Tarayyar 17 daga cikin 24.
A Jihar Adamawa kuwa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ne ke fuskantar barazana daga Aishatu Dahiru Ahmed, ‘yar takarar jam’iyyar APC, inda wasu ke ganin watakila lokaci ya yi da burin mata na zama gwamna a kasar zai cika a wannan karon.
Domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’umma gabani, lokaci da kuma bayan zaben, tuni jami’an tsaron kasar suka kasance cikin shirin ko-ta-kwana don magance duk wani kalubale da zai taso.