✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau Najeriya za ta fafata da Poland a wasan sada zumunta

A yau Juma’a ce kasar Poland za ta kece-raini da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a wasan sada zumunta. Kamar yadda bayanai suka nuna,…

A yau Juma’a ce kasar Poland za ta kece-raini da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a wasan sada zumunta.

Kamar yadda bayanai suka nuna, wasan zai gudana ne a kasar Poland da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya.

kungiyoyin biyu za su hadu da juna ne a shirye-shiryensu na tafiya gasar cin Kofin Duniya da za a yi a Rasha a watan Yuni mai zuwa.

Rahoton ya nuna wasan zai gudana ne a filin wasan da ke daukar ’yan kallo dubu 43 kuma an sayar da tikitin shiga wasan ne a kan kwatankwacin Naira dubu 17.

Tuni kocin Super Eagles ya gayyaci zaratan ’yan kwallo kimanin 23 da yake sa ran da su zai yi amfani a gasar cin Kofin Duniyar.

Poland ta ce za ta yi wasan sada zumunta da Najeriya ce ganin za ta fafata ne a rukunin H da kasashen Kolombiya da Japan da kuma Senegal a gasar cin Kofin Duniya. Ta ce ganin Senegal ta fito daga yankin Afirka ne ya sa ta gayyaci Najeriya don yin wasan sada zumuntar.

Sai dai wasu rahotanni sun nuna kocin Najeriya Super Eagles Gernot Rohr a ranar Talatar da ta wuce ne ya karaya da dan kwallon gaban Poland Robert Lewandowski, inda ya ce babu yadda za a yi ’yan wasan bayan Super Eagles su iya  hana dan kwallon zura kwallo a raga a yayin wasan.  Wannan ta sa wadansu suka rika caccakar kocin da cewa tamkar ya karaya ne tun kafin a yi wasan.

A ranar Talata mai zuwa ce kuma kungiyar Super Eagles za ta sake yin wasan sada zumunta da Serbia. Shi ma wannan wasa za a yi shi ne a shirye-shiryen tunkarar gasar cin Kofin Duniya a Rasha.