Kwamitin alkalai bakwai na Kotun Koli sun fara zaman sauraron shari’ar zaɓen shugaban kasa na 2023 da ake taƙaddama tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar da kuma Peter Obi.
Tun da sanyin safiyar yau Litinin aka tsara matakan tsaro a Kotun Koli gaban fara zama kan shari’ar.
- An Yi Wa Dalibar Kwalejin Ilimi Kisan Gilla A Gombe
- Surukai sun lakada wa malamin Islamiyya dukan da ya yi ajalinsa a Neja
Alkalan karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro sun hadacaa Uwani Abba-Aji, Lawal Garba, Ibrahim Saulawa, Adamu Jauro, Tijjani Abubakar da kuma Emmanuel Agim.
Atiku wanda shi ne babban abokin hamayyar Tinubu daga Jam’iyyar PDP ya daukaka kara zuwa kotun koli ne saboda rashin gamsuwa da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ta kori ƙarar da suka shigar gabanta.
Kotun Koli za ta saurari ɗaukaka karar ne bayan Atiku ya samu kwafin takardun shaidar karatun Tinubu daga Jam’iyyar Jihar Chicago (CSU) da ke kasar Amurka.
Daga cikin bukatun Atiku na soke nasarar Tinubu akwai zargin Shugaba Tinubu da laifin amfani da takardun bogin Jami’ar CSU, zargin da Tinubu ya musanta.
Atiku yana neman gabatar da takardun a matsayin sabbin hujjoji kan dambarwar shaidar karatun Tinubu a gaban Kotun Koli, amma bangaren Tinubu na cewa bakin alkalami ya riga ya bushe, bai kamata a karbi sabbin hujjoji ba da a gabatar da su a kotun baya ba.
Atiku tare da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, sun garzaya kotu ne suna ƙalubalantar nasarar Tinubu a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kowannensu na ikirarin nasara a zaben, wanda Tinubu ya samu kuri’u mafi yawa, Atiku ya zo na biyu, Peter Obi ya zo na uku.
A zaman kotun daukaka kara kan shari’ar, wadda jam’iyyar PDP, LP da kuma DPM ke cikin masu kara, alkalan sun yi watsi da bukatun bangaren masu kara bisa rashin gamsassun hujjoji.