✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau Kotun Koli za ta ci gaba da shari’ar sauyin kudi

Za a ci gaban da shari'a bayan Tinubu mai adawa da sauyin kudi ya ci zaben shugaban kasa.

A safiyar Juma’ar nan ne Kotun Koli za ta ci gaba da shari’a kan dokar sauyin takardun N1,000, N500 da N200 da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sauya wa fasali, wadda gwamnatocin jihohi ke kalubalantar Gwamnatin Tarayya a kai.

Zaman Kotun Kolin a wannan karo na zuwa ne kwana biyu bayan Bola Ahmed Tinubu da ke adawa da sauyin fasalin kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi, ya zama zababben shugaban kasar, kuma za a rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu.

Idan za a iya tunawa dai, an ruwaito Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya kasance dan a-mutum Tinubu, ya ce idan Tinubu ya ci zabe, za a jingine dokar sauyin kudin.

Zaman wannan Juma’ar shi ne na uku da Kotun Kolin take sauraron karar da gwamnatocin jihohi 13, ciki har da na jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya take shugabanci, suna neman kotun ta hana CBN da Gwamnatin Tarayya aiwatar da dokar harramta amfani da tsoffin takardun kudin.

Kwan-gaba-kwan-baya

Idan za a iya tunawa a zaman kotun na karshe, kwmaitin alkalai bakwai da ke sauraron shari’ar sun yi alkawarin kammala shari’ar a ranar, saboda muhimmancin batun sauyin kudin, amma a karshe hakan bai samu ba.

Zaman na wancan karo ya zo ne washegarin bayan zaman Majalisar Koli ta Kasa, inda ta umarci Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya wadata ’yan Najeriya da sabbin takardun N200 da N500 da kuma N1,000 ko kuma ya bari a ci gaba da amfani da tsofaffin har zuwa lokacin da sabbin za su wadata.

Washegari ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya kara wa’adin amfani da tsohuwar takardar N200 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, tsoffin takardun N500 da kuma N1,000 ya ce masu su su kai CBN su ajiye.

Umarnin nasa dai ya fusata ’yan Najeriya dadi, kasancewar tun lokacin da dokokin haramta amfani da tsoffin kudin da kuma takaita cire tsabar kudi suka fara aiki, ake fama da karancin tsabar kudi har a bankuna da cibiyoyin hadahadar kudi, wanda ya haifar da tarzoma da asarar rayuka da kone-kone, musamman a yankin Kudancin kasar.

Hana siyasar kudi

Gwamnatin Tarayya dai ta ce ta sauyin kudin, doka ta tanadi a rika yin sa bayan duk shekara takwas, amma yanzu kusan shekara 20 ba a yi ba a  Najeriya, wanda ya saba wa dokokin manyan bankuna na kasa da kasa.

Ta kara da cewa duk da haka, ta zabi yin hakan a wannan lokaci ne domin talauta ’yan ta’adda da ke ajiye da makudan kudaden da suke karba a matsayin fansar mutanen da ke hannunsu, farfado da darajar Naira, dakile ayyukan masu buga jabun takardun kudin.

Bugu da kari, za ta tilasta wa wadanda suka saci kudi ko suka taskance a gidajensu fitowa da su neman sauyi, bankuna, wanda hakan zai kawo wadatar takardun kudi da ake fama da karancinsu a lokacin bayan.

Sannan dokar takaita cirar kudi za ta dakile siyasar kudi da sayen kuri’u, hana safarar kudaden haram, da kuma ba da damar bibiyar masu tallafa wa ayyukan ta’addanci gami da rage yadda wasu ke taskance tsabar kudi a gidajensu maimakon barin su a bankuna domin amfanin al’umma.

Siyasar canjin kudi

Shari’ar za ta ci gaba ne kwana biyu bayan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu na Jam’iyyar APC mai mulki ya lashe zaben shugaban kasa, ta kuma mika masa takardar shaidar cin zabe.

Tun kafin zaben dai Tinubu, kamar gawamnonin da suka shigar da kara Kotun Koli, ya bayyana adawarsa da dokar sauyin kudin, yana mai bukatar Gwamnatin Tarayya ta tsawaita lokacin amfani da tsoffin takardun kudin da CBN ya sauya wa fasali.

Jagororin APC da magoya bayan Tinubu sun yi zargin cewa sabuwar dokar za ta kawo musu cikas a yakin neman zabe, kasancewar dokar ta fara aiki ne dab da zaben shugaban kasa.

Sai dai kuma an yi ta sa-toka-sa-katsi takanin bankuna da ’yan Najeriya da ke zargin su da boye kudaden da suka ba su, kamar yadda CBN ya ce.

Bankuna dai sun karyata zargin da CBN ke musu, amma daga bisani CBN da Hukumar EFCC suka rika kai samame a bankuna, inda aka rika bankado tsabar sabbin kudaden da suka boye.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an banki sun mayar da sabbin kudin hanyar tatsar masu bukatar, inda suke karbar har kashi 10 zuwa 15 cikin 100 na kudin da mai neman sabbin kudi ta bayan fage yake bukata.

Neman kayar da Tinubu

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa wasu mutane ne a Fadar Shugaban kasa suka kafe cewa sai an yi amfani da dokar, a shirinsu na neman ganin Tinubu ya fadi zaben shugaban kasa.

A cewarsa, mutanen, wadanda bai kama suna ba, sun shirya wa Tinubu makarkashiyar ne saboda wanda suka so ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar (wanda bai bayyana sunansa ba), ya sha kaye a zaben dan takarar shugaban kasa a hannun Tinubu.

El-Rufai, wanda ke sahun gaba wajen shigar da karar a Kotun Koli tare da takwarorinsa na jihohin Kogi da Zamfara, Yahaya Bello da Muhammad Bello Matawalle — kafin sauran jihohi su bi sahu — ya ce sun shigar da kara ne saboda duk kokarinsu na shawo kan Shugaba Buhari ya dakatar da dokar, bai yi nasara ba.

A cewarsa, hakan ta faru ne saboda, duk da wahalar da talakawa ke sha a kan dokar, wadanda yake zargi sun riga sun yi wa Buhari romon baka, kuma ya gamsu cewa abin da aka yi daidai ne, sannan CBN ya ba shi tabbacin cewa zai samar da watatattun takardun kudaden.

Shin Tinubu zai soke dokar

El-Rufai da Matawalle da Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da wasu takwarorinsu dai sun haramta aiki da dokar a jihohinsu, tare da barazanar hukunta duk wanda aka samu yana kin karbar tsoffin kudin.

A yayin da El-Rufai ya umarcin cibiyoyin Gwamnatin Jihar Kaduna su ci gaba da karbar tsoffin kudin, shi da Ganduje sun yi barazanar kwace lasisin duk bankin da ya ki karbar tsoffin kudin.

Idan za a iya tunawa, a wani taron jin ra’ayin al’umma, El-Rufai ya shaida wa jama’ar jihar cewa idan Tinubu ya ci zabe za a ci gaba da amfani da tsoffin kudin da CBN ya sauya wa fasali.

Za kuma a iya tunawa cewa Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani katafaren kantin zamani mai suna WellCare, saboda kin karbar tsoffin kudin.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne hukuncin da Kotun Koi za ta yanke kan wannan shari’a da kuma matakin da sabuwar gwamnati za ta dauka a kan dokar, ganin cewa Bola Tinubu, wanda INEC ta sanar ya ci zaben shugaban kasa, na adawa da dokar.