✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau kotu ke yanke hukuncin zaben Gwamnan Kano

APC na sa ran za a ba wa Gawuna kujerar gwamnan Kano, a yayin da NNPP ke da kwarin gwiwar kotu za ta yi watsi…

Yau daga karfe 8 na safe Aminiya za ta kawo muku rahotanni kai-tsaye daga harabar kotun da ke yanke hukunci kan taddamar zaben gwamnan Jihar Kano na 2023 tsakanin jam’iyyar adawa ta APC da kuma NNPP mai mulkin jihar.

Sai latsa nan domin zuwa shafinmu na kai-tsaye don sanin irin wainar da ake toyawa da zarar kotun ta fara zama.

Bayan da farko ta kammala sauraron bangarorin da ke shari’ar da kuma hujjojinsu, a yau Laraba, 20 ga Satumba, 2023 na Kotu Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Kno za ta yanke hukunci kan karar da APC da dan takarar Nasiru Yusuf Gawuna suka shigar.

Tun a ranar Talata, jajibirin ranar yanke hukuncin aka tsaurara matakan tsaro a yankin da kotun take da wasu sassan Jihar Kano domin tabbatar da doka da oda.

Hakazalika, Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta gargadi jama’a da su guji wuce gona da iri wajen yin murna, bayan kotun ta sanar da hukuncinta.

Karar da aka shigar

Wanda ya zo na biyu a zaben, Nasiru Yusuf Gawuna da jam’iyyar APC sun shigar da kara gaban kotun ne suna kalubalantar nasarar Gwamna Abba Kabir a zaben.

Bangaren Gawuna na zargin Gwamna Abba Kabir da kasancewa ba dan Jam’iyyar NNPP a lokacin da aka tsayar da shi dan takara, don yake ganin takarar ba ta halasta ba, don haka ya kamata kotun ta soke kuri’un da ya samu.

Yana kuma zargin an tafka magudin zabe a wasu wurare da ya shafi kuri’u 130,000, wanda idan aka debe kuri’un da magudin ya shafa, shi ne ya lashe zaben.

Zamam jiran tsammani

A ranar Litinin dai kotun ta sanar da ranar yanke hukuncin, bayan tsawon lokaci ana jiran tsammani, lamarin da ya sa kowanne daga cikin bangarorin da ke shari’ar shirya addu’o’in neman nasara a gaban kuliya.

Ana cikin zaman jiran hukuncin kotun ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sallami wani kwamishinansa saboda yi wa alkalan kotun barazanar kisa, a bisa zargin su da karbar cin hanci da shirin yanke hukuncin da ya dace ba.

Jim kadan bayan kotun ta sanar da ranar yanke hukuncin, bangarorin da ke shari’ar suka nuna cewa suna da kwarin gwiwar samun nasara a kotun.

Za a ba wa Gawuna kujerarsa —APC

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC a Kano, Shehu Maigari, ya ce “bisa ga hujjojin da muka mika wa kotun, muna kyautata zaton za mu yi nasara.

“Ba ma tsoron komai saboda muna da kwarin gwiwa a kan takardun shaida da muka gabatar. Don haka muna da kyakkyawan fata bisa ga abin da muka gabatar.”

Lauyan APC, Offiong Offiong (SAN) ya ce, shaidun da suka gabatar a gaban kotun sun tabbatar da cewa Gwamna Abba ba dan jam’iyyar NNPP ba ne kafin zabe, don haka bai cancanci tsayawa takara ba.

Ya kuma kara da cewa wadanda ake kara sun kasa musanta cewar an yi magudi a wasu takardun zabe sama da 130,000 da aka yi amfani da su wajen bayyana Abba a matsayin wanda ya yi nasara.

A cewarsa, idan aka rage adadin kuri’un da hakan ta shafa, dan takarar APC ne ke da kuri’u mafiya rinjaye.

Kotu za ta kori karar — NNPP

Aminiya ta ruwaito sakataren kungiyar lauyoyin NNPP, Barista Bashir T/Wurzici, yana cewa, “Mun yi farin ciki ranar yanke hukunci ta zo, kuma mun yi farin ciki sosai saboda mun san za a yi watsi da kararsu.

“Muna fatan kotun za ta bi matakin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta bi, saboda lamarin iri daya ne,” in ji shi.

A nasa bangaren, lauyan Gwamna Abba, Adegboyega Awomolo (SAN), ya bayyana cewa shaidu 29 da masu kara suka gabatar, ’yan damfara ne, kuma bai kamata kotun ta yi aiki shaidar da suka bayar ba.

A cewarsa, ya kamata wanda ya shigar da karar ya gabatar da wata hujja a gaban kotun, kamar yadda lauyan NNPP ya gabatar mata da cewa Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa wani daga waje, ba zai iya fada wa NNPP abin da za ta yi ba.

Shugabar kwamitin alkalan mai mutane uku, Mai shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, ta yi alkawarin tabbatar da adalci ga dukkan bangarorin, inda ta ce hukuncin zai zo kafin cikar kwanaki 180 da doka ta ayyana na sauraro da tantance korafin zabe da aka shigar a gabanta.