Wani yaro mai kimanin shekara 10 mai suna Bilya Umaru ya samu kansa a garin Kafanchan bayan sato shi da wadansu mutane suka yi daga Unguwar Shanu-Kaboji da ke karamar Hukumar Mashegu a Jihar Neja.
Lokacin da yake yi wa Aminiya bayani, Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam na karamar Hukumar Jama’a, Alhaji Ilyasu Musa, wanda yaron ke hanunsa, ya ce Bilya ya shaida musu cewa shi makanike ne da ke koyon gyaran babur kafin sato shi da wadansu da ba a san ko su wane ne ba suka yi kafin Allah Ya kubutar da shi.
Alhaji Ilyasu Musa, wanda har ila yau shi ne Mataimakin Jami’in Walwala da Jin Dadin Jama’a na karamar Hukumar Jama’a ya ce, kamar yadda yaron ya shaida masa, ya zagaya ne domin yin fitsari sai kawai ya ji wadansu sun fisgo shi sun saka shi a cikin wata bakar motar kirar Jeep sun yi awon gaba da shi.
Bilya, kamar yadda Alhaji Ilya ya bayyana a gabansa, ya ce daga nan suka bugar da shi ya hau barci bai tashi farkawa ba sai misalin karfe takwas na dare inda ya tsinci kansa a garin Kachia da ke Kudancin Kaduna. “Daga nan sai na roke su a kan ina jin fitsari su bar ni in kewaya. Ina kewayawa sai na gudu inda na shige cikin wata tirela da ke dauke da giya na boye ba tare da sanin direban motar ba,” inji yaron.
Bayan tirelar ta iso garin Kafanchan ta fara sauke kwalaben giya ne kawai sai ga yaron a cikin motar inda ya bayyana wa direban motar labarinsa shi kuma ya kai shi fadar Mai martaba Sarkin Jama’a inda shi kuma ya mika wa kungiyar Jama’atu Nasril Islam.
“Bayan yaron ya fada mana sunan mahaifinsa da sana’arsa da sunan ’yan uwansa sai muka bazama cigiya ta hanyoyi daban-daban har Allah Ya sa aka dace, a ranar Asabar mahaifinsa ya zo muka damka masa shi cikin koshin lafiya.