✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yarinyar da ta bata a Kaduna an gano ta a Maiduguri

Mahaifin yarinyar ya ce 'yar tasa ba ta da isasshiyar lafiya.

An gano wata yarinya mai shekara 13 a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, wadda ta bace kimanin makonni biyu da suka gabata a Jihar Kaduna.

Bayanai sun ce an gano yarinyar ce yayin da take sintiri a titi ba tare da sanin ina ta dosa ba, dalilin ke nan na kama ta kuma aka mika wa ’yan sandan yankin.

Da yake jawabi yayin mika yarinyar ga iyayenta a  ranar Alhamis, mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Borno, ASP Sani Kamilu, ya ce sun yin bincike mai zurfi kafin gano iyayen yarinyar.

Ya ce, “Ta kasance karkashin kulawar CSP Hadiza Musa Sani wanda a ofishinta aka fara gabatar da batun mako biyu da suka shige.”

Mahaifin yarinyar, Ado Usman, ya ce wannan ba shi ne karon farko da ’yar tasa ke bacewa ba saboda rashin lafiya da take fama da ita.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce yarinyar ta kasa ba da bayani kan yadda aka yi ta tafi Maiduguri daga Kaduna.

(NAN)